Home Page
 Tarihin rayuwarsa
   Akidojin Shi'a
   Littafansa
   Fatawoyi
   Sakonni
   Darussa
   Littafan dansa
   Dakin karatu
   Hotuna


Affiliate Websites
Affiliate Websites

   E-Mail Listing:


 

Sakon Ayyatullahi Alnkarani dangane da Kai harinAmerika a Kasar Iraki

Duniyar yau da dukkan musulmi suna cike da bakincikin zalunci Amerika.gwamantin da take da'awar dimokradiyya da Karen hakkin dan  Adam, amma tarihinta yana cike da zalunci ta keta hakkin dan adam.amerika tare da shirin la'ananniyar gwamnatin yahudawan isra'ila, tayi nufin kai haring a kasar musul wato Iraki,don haka dole ne musan gurinsu na asali wanda shi ne,ta wannan hanyar ne Yahudawa zasu samu damar iko akan wurare masu tsarki na ziyara kamar Najaf Da karbala da daui sauransu.Al'ummar duniya a fili suna ganin duk da rashin amincewar al'ummar dduniya tare rashin amincewar majalisar dinkin duniya,amma duk da hakan 'yan koren Isra'ila wato Amerika da Engiland suka samu damar samun ikon  a ksar musulmi kamar Iraki.

 Alummar musulmi Iraki duk da wahala da zaluncin da suka gain da hukumar ba'as ta saddam, haka ma Jamhuriyar musulunci ta Iran ta gabatar da matasanta domin kare musulunci daga zaluncin Saddam har tsawon shekara Takwas,amma har yanzu tana fama da gyaregyaren banna da Saddam ya yi mata tare da Taimakon wadannan Kasashen musamman Amerika. Shin Al'ummar Iraki zasu samu ceto ne daga wadannan ya'n koren Isra'ila ko kuwa su ne da kanasu zasu tashi su nemi hakkinsu?Lallai Amerika ta sani cewa sakamakon wannan zalunci nata ta sa dukkan duniyar musulmi makiyanta kuma masu shirin fito na fito da ita .Haka nan Manyan cibiyoyin nazarin addinin musulunci da manyan malamai na duniyar musulmi da manyan masana na kasashen musulmi suna fata wannan matsala ta kasar Iraki a warwareta ta hanya mai sauki.Amma Amerika wadda take shirin yaki da dukkan kasashen musulmi to lallai su sani kuma tarihin Iraki ya nuna masu cewa al'ummar musulmi ba zasu taba daukar kaskanci da zalunci ba.Sannan Amerika ta sanii ta kawo kanta mahallaka ne da kanta.

 Sannan yah au kan dukkan shuwagabannin kasashen musulmii da su ba wannan matsala muhimmanci har zuwa lokacin da muka ga mutanen Iraki sun fita daga wannan bakin zalunci na Amerika.Nima ta bangarena ina mai bayyanar da bakin cikina dangane da wannan al'amari mai kunar rai,Sannan ina mai neman taimako daga Imamuz-zaman Allah ya gaggauta bayyanarsa don taimakon wadan da aka zalunta.Sannan ya daukaka kalmar musulunci kamar yadda Allah ya yi mana alkawali, kuma hannun Allah yana bias hannnayensu.

 Muhammad Fadhil Lankarani
28-12-1382.Hij.shamsi