Home Page
 Tarihin rayuwarsa
   Akidojin Shi'a
   Littafansa
   Fatawoyi
   Sakonni
   Darussa
   Littafan dansa
   Dakin karatu
   Hotuna


Affiliate Websites
Affiliate Websites

   E-Mail Listing:


 

Annabta

Mun yi imani cewa Annabci aiki ne na Allah Ta'ala, wakilci ne na Ubangiji, wanda shi Allah Ta'ala Yake daukar wadanda Ya zaba daga cikin bayinSa salihai da waliyanSa kamilai a `yan Adamtakarsu, Ya aika su zuwa ga sauran mutane domin shiryar da su ga abinda yake da amfani da maslaha gare su a duniya da kuma lahira. Tare kuma da nufin tsabtace su da tsarkake su daga daudar miyagun dabi'u da munanan al'adu kuma da koya musu hikima da ilimi da bayyana musu hanyoyin Sa'ada da alheri domin `yan Adamtaka ta kai ga kamalarta da ta dace da ita domin ta daukaka ga daraja madaukakiya a gidajen duniya da na lahira
Kuma mun yi imani cewai Lalle ka'idar tausasawa -wanda da sannu za mu yi bayanin ma'anarta nan gaba- ta sanya ya zama babu makawa Allah Ya aiko ManzanninSa domin su shiryar da dan Adam, da kuma isar da sokan gyara domin su zamanto wakilan Allah kuma halifofinSa.
Kamar kuma yadda muka yi imani da cewa Allah Ta'ala bai dora wa mutane hakkin ayyana Annabi ba ko kuma kaddamar da shi ko zaben sa. Ba su da wani zabe a kan haka, sai dai al'amarin haka ga Allah yake domin "Shi ne Ya fi sanin inda zai sa sakonSa." Surar An'am ayata 124. Kuma ba su da wani hukunci a kan wanda Allah zai aiko shi a matsayin mai shiryarwa, mai albishir ko mai gargadi, kamar kuma

yadda ba su da wani hukunci a kan abinda ya zo da shi na daga hakunce-hukunce da sunnoni da shari'a.
 Imam Aliyu Bin Abi Talib (a.s.) yayin da yake bayani ya siffanta fara halitta sama da kasa da halitta Annabi Adam (A.S.) da kuma ambata Annabawa da aiko su ya fada a hudubarsa cewa: "Kuma Subhanu Ya zabi Annabawa daga cikin `ya'yansa (Adam) Ya karbi alkawarinsu a kan wahayi da kuma amanarsu a kan isar da sako. Yayin da yawancin halittunSa suka canja suka jahilci hakkinSa, suka riki ababan bauta tare da Shi shedanu suka fitsare su daga saninSa, suka yanke su daga bautarSa. Sai Ya aiko musu da ManzanninSa, kuma Ya bibiyar musu da AnnabawanSa domin su sake shiryar su ga alkawarin halittarsu, su tunatar da su mantattun ni'imominSa kuma su kafa musu hujja da isar da sako, su farfado da abubuwan da hankali ya mance, su nuna musu ayoyin kudura, na daga rufin da ke dage a samansu, da shinfidar da ke sanye a karkashinsu da abincin rayuwarsu, da ajalin da ke kare su, da gajiya da ke tsofar da su, da faruwar al'amura dake bibiye da su, kuma Allah bai taba barin bayinSa babu Annabi aikakke ko kuma littafi saukakke ba, ko kuma wata hanya bayyananniya ba. Manzanni da karancin mabiya ba ya sa su gaza ko kuma yawan masu karyatawa gare su, duk wanda ya gabata daga cikinsu kan sanar musu wanda zai zo daga bayansa ko kuma wanda ya zo daga baya ya sanar da wanda ya gabance shi. A kan haka karnoni suka yi ta shudewa, zamunna suka yi ta wucewa, iyaye suka yi ta gabata Annabawa suka yi ta biyowa, har Allah subhanahu ya aiko Muhammadu Rasulullahi, sallallahu Alaihi wa alihi, domin aiwatar da alkawarinSa da cika AnnabcinSa da Ya karbi alkawari a gurin AnnabawanSa wanda sunansa mashahuri ne, haihuwarsa kuma mai girma ce. A lokacin mutanen bayan kasa al'ummu ne a rarrabe, masu ra'ayoyin zukata dabam-dabam, da hanyoyi mabambanta, tsakanin masu kamanta Allah da halittunSa, ko kuma wuce iyaka a sunanSa, ko kuma mai nuni zuwa ga waninSa, sai Allah Ya shirye su da shi daga bata, ya tserar da su da kokarinsa daga jahilci." Nahjul Balagha Huduba ta. 1.

Annabci Tausayawane

Lalle shi mutum halitta ne mai haddodi masu ban al'ajabi, mai sarkafaffun gabobi a halittarsa da dabi'arsa da ruhinsa da kuma hankalinsa, kai hatta ma a kan kowane daya daga cikin jama'arsa nauo'in zaburar fasadi sun tattara a cikinsa kamar kuma yadda masu zaburarwa zuwa ga alheri da gyara suka tattara a cikinsa ta bangare gudan.
Allah Ta'ala yana cewa: "Da rayi da abinda Ya daidaita da kuma Ya cusa mata fajircinta da kuma takawarta." (Surar Shamsi: 7-8) "Lalle shi mutum tabbatacce yana c ikin hasara." Surar Asri: 2, da kuma "Lalle ne shi mutum tabbas yana dagawa. Don kawai ganin ya wadata" Surar Alak: 6-7 "Lalle zuciya tabbas mai umarni da mummuna ce". Surar Yusuf: 53. Da sauran ayoyi makamantan wadannan da ke bayyanawa a sarari suna nuni ga irin yadda ran mutum ke kunshe da rauni da kuma sha'awa.
A bangare na biyu kuma, Allah Ta'ala Ya halitta masa hankali mai shiryarwa tare da shi wanda zai kai shi zuwa ga gyara da kuma guraren alheri da kuma zuciya mai gargadi da ke masa fada kada Ya aikata mummuna da zalunci tare da aibata shi a kan aikata abinda yake mummuna abin zargi.
Abokin husumar rai da ke cikin zuciya da imani yana tsakanin aron raunanawa ne da kuma hankali. Duk wanda hankalinsa ya yi galaba a kan rauninsa to yana daga cikin mafi kololuwar matsayi masu shiryarwa a `yan adamtakarsu, kammalallau a ruhinsu wanda kuwa rauninsa ya rinjaye shi to lalle yana daga cikin masu hasarar matsayi, masu taraddudi a yan Adamtaka, masu faduwa zuwa matsayin dabbobi.
Mafi tsanani daga cikin wadannan masu husuma biyu itace tausasawar zuciya da rundunarta. Don haka ne kake ganin yawancin mutane sun dulmuye a cikin bata, suna nesa da shiriya ta hanyar bin sha'awace-sha'awace da amsa kiran raunin zuciya, "kuma mafi yawan mutane ba za su zama muminai ba koda kuwa ka yi kwadayin haka." Surar Yusuf 103.
Shi mutum saboda gazawarsa da rashin saninsa game da abubuwan da ke kewaye da shi, da kuma rashin sanin asirran abubuwan da ke kewaye da shi da ma wadanda ke bullowa daga cikinsa shi kansa, ba zai iya sanin dukan abinda zai cutar da shi ko ya amfane shi ba shi da kansa, ba kuma zai iya sanin abinda zai kai shi ga samun sa'ada ko ya kai shi ga tsiyacewa ba, sawa'un a kan abinda ya kebatu da shi ne shi kadai ko kuwa wanda ya shafi dan Adam baki daya da kuma al'ummar da ke kewaye da shi. Shi bai gushe yana jahili kuma yana kara jahilci ne ko kuma kara fahintar jahilcinsa ne duk yayin da iliminsa game da dabi'a ko kuma ababan halitta ya kara karuwa. Saboda haka mutum a tsananin bukatarsa ta son kaiwa ga darajar sa'ada yana bukatar wanda zai dora shi a kan hanya mikakkiya shararriya zuwa ga shiriya domin rundunar hankali ta kara karfafa da haka har ya zamanto mutum zai iya yin galaba a kan abokin gabarsa yayin da ya shiga fagen faman gwabzawa tsakanin rundunar hankali da raunin tausasawar zuciya.
Yawanci bukatar wanda zai kama hannunsa zuwa ga alheri da gyara na kara tsananta ne yayin da tausasawar zuciya ke yaudarar sa ta hanyar nuna masa abinda yake mummuna cewa mai kyau ne ko kuma kyakkyawa cewa mummuna ne ta nuna masa kyawun fandarewarsa, ta rikitar masa hanyar gyara da sa'ada da ni'ima a lokacin da shi ba shi da masaniyar da zai bambance dukan abinda yake mai kyau mai amfani da kuma wanda yake mummuna marar amfani ga mai gaggawar kutsawa cikin wannan arangamar ne ta yadda ya sani ko kuma ta inda bai sani ba sai dai wadanda Allah Ya kubutar.
Saboda haka abu ne mawuyaci ga mutum masanin ilimin zamani ya kai kansa ga dukan tafarkunan alheri da amfani da kuma sanin dukan abinda zai amfane shi ko ya cutar da shi a duniya da lahira ballantana kuma jahili; sawa'un al'amari ne da ya kebe shi shi kansa ko kuma ya hada da al'umma da yake zaune a cikinta ne. Ba ya taba kaiwa ga wannan masaniyar koda kuwa ya hada kai ya yi taimakekeniya da sauran mutane da ke tare da shi ko da kuwa sun hadu sun yi bincike, koda kuwa sunyi tarurruka da zama dabam-dabam da kuma shawarwari.
Don haka ne ya zama wajibi Allah Ta'ala Ya aiko da Annabawa da manzanni a cikin mutane domin rahama da tausasawa gare su. "Manzo daga cikinsu yana karanta musu ayoyinSa yana tsarkake su kuma yana koya musu littafi da hikima" (Surar Juma'a: 2). Yana musu gargadi game da abinda ke da cutarwa gare su kuma yana musu albishir game da abinda yake da alheri da gyaruwa da sa'ada a gare su. Tausasawar daga Allah wajibi ne domin tausasawa ga bayinSa na daga cikin tsantsan kamalarSa. Shi mai tausasawa ne ga bayinSa, Mai yawan baiwa, Mai karimci, idan kuwa har ya zamanto a wani guri da ya dace akwai bukatar Ya kwarara kyautarSa da tausasawa to babu makawa Ya zuba tausasawarSa domin babu rowa a farfajiyar rahamarSa, babu nakasa da tawaya a kyautarSa da karimcinSa.
Ma'anar wajibi a nan ba wai tana nufin cewa wani zai umarce shi da aikata haka ba ne har Ya zama tilas a kansa Ya yi wa wanda Ya yi umarni biyayya! Allah Ya daukaka ga haka, ma'anar wajibi a nan tamkar ma'anar fadin da ake yi ne cewa shi Allah wajibin samamme ne wato ba zai taba koruwa ba ba zai taba yiwuwa a raba shi da samuwa ba.

Mu'ujizar Annabawa

Mun yi imani da ccwa lalle Allah Ta'ala tunda Yake sanya wa bayinsa mai shiryarwa da kuma Manzo to babu makawa Ya sanar da shi gare su, Ya kuma nuna musu ko wane ne shi a ayyane. Wannan kuwa ya takaita ne a kan sanya musu wani dalili da kuma kafa musu hujja a sakon domin cika tausasasarSa da kuma kammala rahamarSa.
Allah Ta'ala Yana cewa: "Manzanni masu bushara da kuma gargadi domin kada mutane su zama suna da wata hujja a gurin Allah bayan Manzanni kuma Allah Mabuwayi ne Mai hikima." Surar Nisa'i: 165.
Wannan, kafa hujjar kuwa babu makawa ya ramanto irin wanda ba ya samuwa sai daga mahaliccin halittu, mai sarrafa samammu- wato ya zamanto abin ya dara kudurar dan Adam. Ya sanya shi a hannun shi manzon mai shiryarwa, domin ya zamanto an san shi da shi kuma ya zamanto mai shiryarwa zuwa gare shi wannan dalili da hujja shi ake kira mu'ujiza; wato gagara badau saboda kasancewarsa ya gagari dan Adam, ya yi gasa da shi ko kuma ya kawa makamancinsa.
Kamar yadda babu makawa ga Annabi ya zo da mu'ujiza ya bayyana ta ga mutane domin ya kafa musu hujja haka nan babu makawa wannan mu'ujizar ya nuna ta kuma yadda za ta gagari malamai da kuma kwararrun zamaninsa; ballantana kuma sauran mutane, tare kuma da danganta wannan mu'ujizar da ikrarin Annabci daga mai mu'ujizar, saboda kasancewarsa yana da sadarwa ruhi da wanda yake jujjuya halittu.
Idan wannan ya tabbata ga mutum, bayyanar mu'ujiza wadda ta saba wa al'ada, ya kuma yi da'awar Annabci da sako, to a lokacin sai ya zamanto abin gaskatawar mutane a kiran da yake yi, tare da yin imani da sakon nasa, da bin maganarsa da umarninsa, sai wanda zai gaskata shi Ya yi imani da shi wanda zai ki kuma ya kafirce masa.
Wannan shi ne abinda ya sa muka ga cewa mu'ujizar kowane Annabi ta dace da ilimi da kuma fasahar zamaninsa. Mu'ujizar Annabi Musa ita ce sanda wanda ke hadiye sihiri da abinda suke yin ba duhunsa saboda kasancewar sihiri a zamaninsa shi ne fannin fasaha da yake mashahuri yayin da sandan ya zo sai dukan abinda suke aikatawa ya baci suka san cewa lalle wannan abu ne da ya fi karfinsu kuma ya dara irin fannin fasaharsu, lalle wannan yana daga cikin abubuwan da, dan Adam ya gaza ya kawo shi kuma kwarewa da ilimi sun dushe a gabansa. Allah Ta'ala yana cewa: "Kuma sai muka yi wahayi ga Musa kan cewa jefa sandanka sai ga shi yana hadiddiye abubuwan da suke kirkirawa. Kuma gaskiya ta tabbata abinda suke aikatawa kuma ya baci. Sai aka rinjaye a nan ,sa'annan suka koma suna kaskantattu. Kuma aka kifarda masu sihirin suna sujada." Surar A'araf: 117-120.
Hakanan mu'ujizar Annabi Isa (A.S.) ita ce warkar da makafi da masu albaras da kuma raya matattu saboda shi ya zo ne a lokacin da likitanci shi ne fannin fasahar kwarewar da ke tsakanin mutane kuma akwai malamai akwai likitoci da suke su ne manyan bokaye gare su sai iliminsu ya gaza jeruwa da abinda Annabi Isa (A.S.) Ya zo da shi. Allah Ta'ala Yana cewa: "Kuma Manzo zuwa ga Bani Isra'ila cewa lalle ni na zo muku da aya daga Ubangijinku ni ina halitta muku daga laka abinda yake kamar surar tsuntsu kuma in hura a cikinsa ya zamanto tsuntsu da izinin Allah kuma ina warkar da makaho da mai albaras kuma ina raya mamata da izinin Allah kuma ina ba ku labarin abinda kuke ci da wanda kuke taskancewa a gidajenku lalle a cikin wannan akwai aya gare ku idan kun kasance muminai." Surar Al- Imran: 49.
Mu'ujizar Annabinmu madawwamiya ita ce Alkur'ani saboda shi ya zo ne a lokacin ma'abuta ilimin balaga su ne kan gaba a tsakanin mutane inda ya kure su da balagarsa da bayaninsa. Duk da fasaharsu da balagarsu sai da Alkur'ani ya kaskantar da su ya rikitar da su ya fahintar da su cewa su ba za su iya fito na fito da shi ba don haka suka sallama masa rinjayayyu bayan sun gaza kasawa da shi, suka ma gaza isa ga kurar da ya tile su da ita ya wuce ya barsu.
Allah Ta'ala yana cewa: "Kuma idan da mutane da Aljannu za su taru a kan su zoda kwatankwacin wannan Alkur'anin to da ba za su zo da makamancinsa ba koda kuwa sashensu na taimakon sashe." Surar Isra'i: 88.
Kalubalantar su da ya yi kan cewa su kawo sura goma suka kasa na tabbbatar da cewa lalle ya gagare su. Allah Ta'ala Yana cewa: "Ko suna cewa shi ne ya kage shi ne ka ce to ku zo da surori goma makamantansa kagaggu kuma ku kira duk wanda za ku iya wanda ba Allah in kun kasance masu gaskiya" Surar Hud: 13
Sa'an nan kuma ya sake kalubalantar su kan su kawo sura guda kamar sa suka gaza. Allah Ta'ala Yana cewa: "Kuma idan har kun kasance a cikin kokwanto daga abinda muka saukar to ku zo da sura guda kamar sa kuma ku kira shaidunku da ba Allah ba in kun kasance masu gaskiya". Surar Bakara: 23
Allah Ta'ala Yana cewa: "Ko suna cewa ya kage shi ne ka ce ku zo da sura guda kamarsa kuma ku kira duk wanda za ku iya ba Allah in kun kasance masu gaskiya". Surar Yunus: 38.
Ya sanar da mu yadda suka koma fito na fito da hakora ba da harshe ba Ya sanar da mu cewa shi Alkur' ani wani nau'i ne na mu'ujiza kuma Annabi Muhammad bin Abdullah ya zo da shi ne da kira da kuma da'awar sako. Don haka muka san cewa Manzon Allah (S.A.W.A.) ya zo da gaskiya da hakika kuma shi ma ya gaskata da shi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.

 Ismar Annabawa

Kuma mun yi imani da cewa Annabawa ma'asumai ne, ba sa aikata sabo dukkaninsu kazalika Imamai kyakkyawar gaisuwa ta tabbata a gare su. Mun saba da wasu daga cikin musulmi a kan haka don su ba su wajabta isma (rashin aikata sabo) ga Annabawaballantana ma Imamai.
Isma: Ita ce tsarkaka daga aikata zunubi da sabo kananansu da manyansu; da kuma tsarkaka daga mantuwa , koda kuwa hankali bai kore aukuwar haka daga Annabi ba. Sai dai kawai wajibi ne ya zamanto ya tsarkaka hatta daga dukkan abinda ke zubar da mutunci kamar cin abu a kwararo a tsakanin mutane ko kuma kyalkyala dariya da dai dukkan abinda bai dace a aikata shi ba a tsakanin mutane ba.
Dalilin da ya sa Isma ta zama wajibi kuwa shi ne idan da har ya halatta Annabi ya aikata sabo ko kuma ya yi kuskure, ko kuma wani abu makamancin wannan ya auku daga gare su to kuwa lalle da biyayya gare su a aikin da suka aikata da sabo ko kuskure bai wajaba ba, ko kuma da idan har ya wajaba to da mun halatta aikata sabo da dogaro da rangwame daga Allah, bilhasali ma dai mun wajabta haka ne wannan kuwa abu ne tabbatacce a wajiban addini da kuma a gurin hankali.
Idan kuwa biyayya gare shi bata wajaba ba a kan haka to kuwa wannan ya saba wa annabci wanda babu makawa tana tare da wajabcin da'a dimin da'iman. Idan kuwa ya zamanto duk abinda ya auku daga gare shi muna jin cewa imma daidai ne imma kuskure to bai wajaba a yi masa da'a a kan kome ba, sai fa'idar aiko Annabawa ta zamanto ta tafi haka nan kawai Annabin kuma sai ya zama kamar sauran mutane, maganarsa ba ta da wata kimar da za a dogara a kanta da'iman kamar yadda biyayya gare shi ba za ta zama tilas ba. Ba ma za a sami kwanciyar hankali ba baki daya game da maganganunsa da ayyukansa.1
Wannan kuma dalili ne da ke tabbatar da cewa Isma na tare da Imami domin kaddara cewa shi zababbe ne daga Allah Ta'ala don shiryar da mutane a matsayin halifan Annabi. Za mu yi karin bayani a fasali game da Imamah.
 A duba sharhin al-Makasid Juzu'i na 5 shafi na 50, da kuma al-Ganiyyatu fi Usuluddin shafi na 161.
Sayyid Murtadha ya ambata a cikin littatin Tanzihil Anbiya da nassi kamar haka: "Asahabul Hadis da Hashwaiyawa sun halatta wa Annabawa aikata manyan zunubai kafin a ba su Annabci. Daga cikinsu ma har akwai wadanda suka halatta wa Annabawa aikata sabo hatta bayan karbar Annabcin in banda karya a kan al'amuran shari'a, akwai ma wadanda suka halatta karyar amma da sharadin a boyewa ba bayyanawa ba, akwai ma wadanda suka halatta a kowane hali, su Mu'utazilawa kuwa sun haramta cewa Annabawa na aikata sabo babba ko karami kafin annabci da kuma bayan ba su annabcin amma sun halatta aukuwar abinda bai kai karamin zunubi ba gare su kafin annabci da kuma bayan annabcin amma sun yi sabani a kan Shugaban Manzanni Muhammadu (S.A.W.A.) wasu sabi daga cikinsu akwai wadanda suka ce zai iya aikata kananan ayyukan sabo haka nan da gangan, daga cikinsu kuma akwai wadanda suka ce ata tau sam annabawa ba sa taba aikata wani abu da suka san cewa sabo ne sai dai kawai fuskar ba shi wata ma'ana ta dabam. An hakaito daga Nizam da Ja'afar Bin Mubasshir da kuma wasu jama'a da suka bi su a kan cewa aikata sabo daga gare su ba ya yiwuwa sai dai a kan mantuwa da rafkanuwa kuma za a kama su da haka koda kuwa an yafewa al'ummunsu saboda karfin saninsu da kuma martabarsu.Tanzihul Anbiya: Gabatarwa.
 Ma'anar Isma a luga ita ce: Abu da ke kange mutum daga wani abu wato kamar ya kange shi daga aukuwar wani abu da ba ya so. Akan ce wane ya yi isma da dutse idan ya yi kariya da shi, da haka ne ake kiranta Isma wato fakewa a dutse don kariya da shi, ya zo a Lisanil Arab cewa: "Isma ita ce kariya, a kan ce na kare wani sai ya karu, na yi kariya da Allah idan har ya tsaru daga sabo da tausasawarSa.
Isma daga Allah Ta'ala kuwa ita ce: Muwafaka da ke kubutar da mutum daga abinda da ya so idan har ya zamanto ya aikata aikin biyayya, kamar yadda muke mika igiya ga mutumin da kogi yake kokarin dulmuyarwa ya kama ya tsira da ita, Allah Ta'ala ya bayyana wannan ma'ana a littafinSa da cewa: "Ku yi riko da igiyar Allah baki daya" Surar Ali Imran: 103. A nan abin nufi da igiyar Allah shi ne addininsa.
Ya zo daga Imam Zainul Abidin (A.S.) cewa yayin da aka tambaye shi ma'anar ya ce: Shi ne mai riko da igiyar Allah, igiyar Allah kuma shi ne Alkur'ani da Imam, ba sa taba rabuwa har zuwa ranar tashin kiyama, Imam yana shiryarwa ne zuwa ga Alkur'ani shi ma Alkur'ani yana shiryarwa zuwa ga Imam. Wannan shi ne fadin Allah Ta'ala: "Lalle ne shi wannan Alkur'ani yana shiryarwa zuwa ga wadanda suke su ne mafiya daidai " Surar Isra'i: 9.
Biharul Anwar Juzu'i na 25 shafi na 194 da kuma farko al-Makalat na Shaikh Mufid Juzu'i na 4 shafi na 34. Da kuma Lisanul Arab Juzu'i na 12 shafi na 403 bayani game "Asama".
1- Domin a cikin yin haka akwai kore ayar Alkur'ani wadda take kwadaitarwa da a yi biyayya ga Manzon Allah (S.A.W.A.) cewa: "Kuma wanda ya bi Allah da ManzonSa zai shigar da shi gidajen Aljanna wadanda koramu ke gudana a karkashinsu." Surar Nisa'i: 13. da kuma fadin Allah Ta'ala cewa: "Kuma wanda ya bi Allah da Manzon to wadannan suna tare da wadanda Allah ya yi ni'ima gare su," Nisa'i: 69 da kuma fadinsa cewa: "Kuma wanda ya bi Manzon Allah to Lalle ya bi Allah ne" surar Nisa'i: 80 da kuma: "Lalle hakika gare ku daga Manzon Allah akwai kyawawan abin koyi ga duk wanda ke kaunar Allah da ranar Lahira kuma ya ambaci da yawa" Surar Ahzab: 22 da kuma fadin Allah Ta'ala: "Kuma wanda ya bi Allah da ManzonSa to lalle ya rabbonta da rabo mai girma". Surar Abzab: 71.
- Domin a cikin yin haka akwai kore ayar Alkur'ani da ke kwadaitar da biyayya ga Manzon Allah (S.A.W.A.) cewa: "Kuma wanda ya bi Allah da ManzonSa zai shigar da shi gidajen Aljanna da koramu ke gudana a karkashinsu." Nisa'i: 13
"Kuma wadanda suka yi da'a ga Allah da ManzonSa to wadan suna tare da wadanda Allah ya yi ni'ima gare su". Surar Nisa'i: 69.

Siffofin Annabi


Mun yi imani da cewa, Annabi kamar yadda ya wajaba ya zamanto ma'asumi haka nan ya wajaba ya zamanto yana da mafi kamalar siffofin dabi'u da hankali wadanda mafifita sune jarumtaka, da iya tafida jama'a, da shugabanci da hakuri, da karfin kwakwalwa da hazikanci, har ya zamanto babu wani daga cikin mutane da zai yi kusa da shi a kan haka, domin ba don haka ba da babu yadda Annabcin ya zamanto al'amuran duniya baki daya ba. shugabaci a kan dukan halittu kamar kuma yadda ba zai yiwu ya zamanto ya tafi da
Kazalika wajibi ne ya zamanto mai tsarkin haihuwa dan halas, amintacce, mai gaskiya wanda yake tsarkakakke daga dukkan miyagun dabi'u hatta kafin aiko shi saboda zukata su amintu da shi rayuka kuma su juya zuwa gare shi hatta ma don ya cancanci wannan matsayi mai girma daga Ubangiji.

 Annabawa da Littafansu


Mun yi imani a dunkule da cewa dukkan Annabawa da Manzanni a kan gaskiya suke, kamar yadda muka yi imani da kasancewarsu ma'asumai tsarkakakku. Musanta Annabcinsu kuwa, da zaginsu, da yin izgili da su yana daga kafirci da zindikanci, domin yin haka yana nufin karyata Annabinmu wanda Ya ba da labari game da su da kuma game da gaskiyarsu.
Wadanda aka sani daga cikinsu kuwa kuma aka san shari'o'insu kamar Annabi Adam (A.S.) da Annabi Nuhu (A.S.) da Annabi Ibrahim (A.S.) da Annabi Dawud (A.S.) da Annabi Sulaiman (A.S.) da Annabi Musa (A.S.) da Annabi Isa (A.S.) da sauran Annabawan da Alkur'ani ya ambace su a sarari ya wajaba a yi imani da su a ayyane duk kuwa wanda ya karyata daya daga cikinsu to ya karyata su baki daya kuma ya karyata Annabinmu a kebance.
Kazalika ya wajaba a yi Imani da littafansu da abinda aka saukar musu.
Attaura da Linjila ko kuma Bebul Tsoho da Sabon Alkawarin da ke hannun mutane a wannan zamanin ya tabbata cewa gurbatattu ne daga ainihin wadanda aka saukar saboda abinda ya auku gare su na daga canje-canje da musanyawa, na daga kari da ragi bayan zamanin Annabi Musa da Annabi Isa (A.S.) saboda wasan da ma'abuta son rai da kwadayi suka yi da su. Bilhasali ma dai yawanci ko kuma ma dukkaninsu mabiya ne suka kaga su; bayan su Annabi Musa (A.S.) da Annabi Isa (A.S.) ba sa nan.
____________
 "Ku ce mun yi imani da Allah da abinda aka saukar gare mu da abinda aka saukar zuwa ga Ibrahima da Isma'ila da Ishaka da Yakuba da Jikoki da abinda aka ba wa Musa da Isa da abinda aka ba wa Annabawa daga Ubangijinsu, ba ma rarrabewa a tsakanin kowa daga cikinsu kuma mu masu sallamawa ne a gare shi." Surar Bakara: 136
"Amma tabbatattu a cikin ilimi daga cikinsu da muminai, suna imani da abin da aka saukar zuwa gare ka da abinda aka saukar kafin kai kuma suna masu tsai da salla suna ba da zakka suna masu imani da Allah da ranar lahira wadannan za mu ba su lada mai girma" Surar Nisa'i: 162.
    Ya zo a ruwayoyi da hadisai cewa adadin Annabawa ya kai dubu dari da ashirin da hudu da dari uku da ashirin da uku daga cikinsu ne, ko kuma dari uku da ashirin da biyar a bisa sabanin ruwaya, su kuma wadannan Annabawan sunan mafi yawansu bai zo a Alkur'ani ba. Allah Ta'ala na cewa: "Kuma lalle hakika mun aika wasu Manzannin kafin kai, daga cikinsu akwai wadanda muka ba ka
labarinsu daga cikinsu akwai wadanda ba mu ba ka labarinsu ba" Surar Ghafir: 78.
Adadin wadanda sunansu yazo a Alkur'ani kuwa ashirin da shida ne kamar haka:-
1- Annabi Adam (A.S.): sunansa ya zo sau 18 a Alkur'ani, game da shi Allah Ta'ala yana cewa: "Lalle Allah ya zabi Adama da Nuhu da zuriyar Ibrahim da zuriyar Imran a kan dukkan talikai." Surar Al- Imran 33, Kamar Kuma yadda ya zo da Kiran Bani Adam sau Bakwai,
2- Annabi Nuhu (A.S.): sunansa ya zo a Alkur'ani sau 43, game da shi Allah Ta'ala yana cewa: "Kuma lalle Mun aika Nuhu zuwa ga mutanensa ya zauna a cikinsu har shekaru dubu babu hamsin" Surar Ankabutu: 14.
3- Annabi Idris (A.S.): sunansa ya zo sau biyu a Alkur'ani, Allah Ta'ala Yana cewa: "Kuma ka ambata Idris a cikin littafi Lalle shi ya kasance mai yawan gaskiya Annabi" Surar Maryam: 56.
4- Annabi Hudu (A.S.): Sunansa ya zo sau goma a cikin Alkur'ani, game da shi Allah Ta'ala na cewa: "Kuma zuwa ga Adawa dan'uwansu Hudu, ya ce ya mutanena ku bauta wa Allah, ba ku da wani abin bautawa baicin Shi." Surar A'araf: 69 da Surar Hudu: 50.
5- Annabi Salihu(A.S.): Sunansa ya zo sau tara a Alkur'ani, game da shi Allah Ta'ala Yana cewa: "Kuma lalle Mun aika wa Samudawa dan'uwansu Salihu ku bauta wa Allah sai suka zamanto bangarori biyu suna husuma." Surar Namli: 45.
6- Annabi Ibrahim(A.S.): Ambaton sunansa ya zo sau 69 a Alkur'ani, game da shi Allah Ta'ala Yana cewa: "Kuma lalle Mun aika Ibrahima kuma Muka sanya Annabci da littafi a zuriyarsu..." Surar Hadid: 26.
7- Annabi Ludu(A.S.): sunansa ya zo a gurare 26 a Alkur'ani, game da shi Allah Ta'ala yana cewa: "Kuma lalle Ludu tabbas yana daga Manzanni". Surar Saffat: 133.
8- Annabi Isma'il(A.S.): Ambaton sunansa ya zo a gurare goma sha daya a Alkur'ani, game da shi Allah Ta'ala Yana cewa: "Kuma Muka yi wahayi zuwa ga Ibrahima da Isma'ila da Ishaka da Yakuba..." Surar Nisa'i: 163.
9- Alyasa'u(A.S.): Ambaton sunansa ya zo sau biyu a Alkur'ani, game da shi Allah Ta'ala Yana cewa: "Da Isma'ila da Alyasa'u da Yunusa da Ludu kuma kowanne Mun fifita shi a kan talikai."
10- Zulkifli(A.S.): An ambace shi sau biyu a Alkur'ani. Allah Ta'ala Yana cewa: "Kuma ka ambaci Isma'ila da Alyasa'u da Zulkifli kuma duka suna daga zababbu." Surar Sad: 48
11- Annabi Ilyasu (A.S.): An ambace shi sau biyu a Alkur'ani, Allah Ta'ala Yana cewa: "Kuma lalle Ilyasu tabbas na daga cikin manzanni." Surar Saffat: 123.
12- Annabi Yunus (A.S.): Ambatonsa ya zo sau hudu a Alkur'ani. Allah Ta'ala yana cewa: "Kuma lalle Yunusa Tabbas yana daga cikin Manzanni." Surar Saffat: 139.
12- Ishak (A.S.): Ambaton sunansa ya zo sau goma sha bakwai a Alkur'ani. Allah Ta'ala Yana cewa: "Kuma mun yi Masa albishir da Ishaka Annabi daga cikin Salihai." Surar Saffat: 112.
14- Annabi Yakub (A.S.): An ambaci sunansa sau goma sha shida a Alkur'ani. Allah Ta'ala Yana cewa: "...Kuma Muka yi wahayi ga Ibrahima da Isma'ila da Ishaka da Yakuba da Asbata da Isa..." Surar Nisa'i: 163
15- Annabi Yusuf (A.S.): Ambatonsa ya zo sau ashirin da bakwai a Alkur'ani. Allah Ta'ala Yana cewa: "Kuma daga cikin zuriyarsa akwai Dawuda da Sulaimanu da Ayyuba da Yusufa da Musa da Haruna kuma haka nan Muke sakamtawa masu kyautatawa." Surar An'am: 84.
16- Annabi Shu'aib (A.S.): Sunansa ya zo sau goma sha daya a Alkur'ani. Game da shi Allah Ta'ala Yana cewa:"Kuma ga Madyana dan'uwansu Shuaibu." Surar A'araf: 85, Hud: 84, Ankabut: 36.
17- Annabi Musa (A.S.): Ambatonsa ya zo sau dari da talatin da shida a Alkur'ani. Game da shi Allah Ta'ala Yana cewa: "Kuma lalle tabbatacce Mun aiki Musa da ayoyinMu kan cewa ka fitar da al'ummarka daga duffai zuwa ga haske kuma ka tunatar da su game da ranakun Allah lalle a cikin wannan akwai ayoyi ga dukkan mai hakuri mai yawan godiya." Surar Ibrahim: 5.
18- Annabi Haruna (A.S.): Ambaton sunansa ya zo sau ashirin a Alkur'ani. Allah Ta'ala yana cewa: "Kuma Muka ba shi Dan'uwansa Haruna Annabi daga rahamarMu." Surar Maryam: 53.
19- Annabi Dawud (A.S.) Ambatonsa ya zo sau goma sha shida a Alkur'ani. Allah Ta'ala Yana cewa: "Da Ayyuba da Yunusa da Haruna da Sulaimana kuma Mun ba wa Dawuda Zabura." Surar Nisai: 163.
20- Annabi Sulaiman(A.S.): Ambatonsa ya zo sau goma sha bakwai a Alkur'ani. Allah Ta'ala Yana cewa: "Kuma lalle hakika Mun ba wa Dawuda da Sulaimanu ilimi" Surar Namli: 15.
21 - Annabi Ayyuba (A.S.): An ambace shi sau hudu a Alkur'ani. Game da shi Allah Ta'ala Yana cewa: "Ibrahima da Isam'ila da Ishaka da Ya'akuba da Asbata da Isa da Ayyuba." Surar Nisa'i: 163.
22- Annabi Zakariyya (A.S.): Ambatonsa ya zo sau bakwai a Alkur'ani. Game da shi Allah Ta'ala Yana cewa: "Da Zakariyya da Yahya da Isa da Ilyasu kowane yana daga Salihai" Surar An'am: 85.
23- Annabi Yahya (A.S.): Sunansa ya zo sau biyar a Alkur'ani. Game da shi Allah Ta'ala Yana cewa: "Ya Yahya ka riki littafi da karfi kuma Mun ba shi hukunci yana yaro." Surar Maryam: 12.
24- Annabi Isma'ila Sadikul Wa'ad (A.S.): shi wani Isma'ilan ne dabam banda dan Annabi Ibrahim (A.S.). Game da shi Allah Ta'ala yana cewa: "Kuma ka ambaci Isma'ila a cikin littafi lalle shi ya kasance mai gaskiyar alkawari kuma ya kasance Manzo Annabi." Surar Maryam: 54.
25- Annabi Isa (A.S.): Sunansa ya zo sau ashirin da shida a Alkur'ani. Game da shi ne Allah Ta'ala Yake cewa: "Lalle abin sani kawai shi ne cewa Al-Masihu Isa dan Maryama Manzon Allah ne kuma KalmarSa. Ya jefa ta zuwa ga Maryama..." Surar Nisa'i: 171.
26- Annabi Muhammadu (S.A.W.A.): Ambatonsa da sunan Muhammad ya zo sau hudu a Alkur'ani, da Ahmad kuma ya zo sau daya. "Kuma Muhammadu bai kasance ba face Manzo kuma Manzanni sun gabata kafin shi." Surar Al-Imran: I 44.
Daga cikin Annabawa akwai wadanda aka kawo siffofinsu ba sunayensu ba a Alkur'ani. Allah Ta'ala na cewa: "Shin ba kaga wasu mashawarta ba daga Bani Isra'ila bayan Musa, yayin da suka ce ga wani Annabinsu, nada mana wani sarki mu yi yaki a tafarkin Allah". Surar Bakara: 246.
Su Manzannin an rarraba su ne an aika su zuwa ga al'ummu dabam daban a zamunna dabam-daban. Allah Ta'ala Yana cewa: "Kuma lalle hakika Mun aika Manzo ga kowace al'umma". Surar Nahl: 36.
Wasu Annabawa da Manzannin kuma an fifita su a kan wasu: Allah Ta'ala Yana cewa: "Wadancan Manzannin Mun fifita wasunsu a kan wasu daga cikinsu akwai wanda Allah Ya yi masa magana; kuma Ya daukaka sashensu a daraja." Surar Bakara: 253
"Kuma lalle hakika Mun fitita wasun Annabawa a kan wasu kuma Mun ba wa Dawuda Zabura." Surar Isra'i: 55.
Mafifita daga cikin Annabawa da Manzanni su ne Ulul Azami su biyar wadanda game da su Allah Ta'ala ke cewa: "Kuma yayin da Muka karba daga Annabawa alkawarinsu da kuma daga gare ka da kuma daga Nuhu da Ibrahima da Musa da Isa Dan Maryama kuma Mun karba daga gare su alkawari mai tsanani." Surar Ahzab: 7.
 
"Don haka ka yi hakuri kamar yadda ma'abuta karfin himma daga Manzanni suka yi hakuri." Surar Ahkaf: 35.
Kuma sananne ne cewa himmar Annabawa ta sha bamban, ba daya take ba a gurin dukkaninsu kamar yadda Allah Ta'ala ke bayyana haka da cewa: "Kuma lalle hakika mun yi alkawari ga Adam kafin wannan sai ya manta kuma ba Mu sami karfin himma gare shi ba." Surar D.H.: 115.
Mafificin Annabawa da Manzanni baki daya shi ne cikamakinsu, Annabi Amintacce Muhammad Dan Abdullahi (Tsira da Amincin Allah su tabbata gare shi da zuriyarsa tsarkakku). A duba Biharul Anwar Juzu'i na ll shafi na 77 da kuma Alkhisal. Al- Amali Shaikh Mufid, da Kanzul Ummal, 32276, 32277, 32282, da sauransu, da Tafsirin Al- Mizan Juzu'i na 2, da Mizanil Hikma Juzu'i na 7 da dai sauransu

Takaicen tarihin Manzo s.a.w.a

Sunansa da nasabarsa :Muhammad dan Abdullahi dan Abdulmudallibi dan Hashimi dan Abdu manafi dan kusayyi dan kilabi, nasabarsa madaukakiya tana tukewa zuwa ga annabi Ibrahim (AS).

Mahaifiyarsa :ita ce Aminatu ‘yar wahabi dan Abdu Manafi dan Zuhrata dan kilabi.

Alkunyarsa :Abul kasim, Abu ibrahim.

Lakabinsa :Almusdafa , yana da sunaye da suka zo a cikin  alkur’ani mai girma kamar:khataman nabiyyin, Al’ummi , Almuzammil , Almudassir , Annazir , Almubin , Alkarim , Annur , Anni’ima , Arrahma , Al’bdu , Arrauf , Arrahim , Asshahid , Almubasshir ,Annazir , Add’ai da sauransu.

Tarihin haihuwarsa:17 Rabiul auwal shekarar giwa(571m)bisa mashhurin zance gun shi’a, an ce 12 ga watan da aka ambata.

Wurin haihuwarsa:Makka.

Aikoshi :an aiko shi a Makka 27 rajab yana dan shekara arbain.

Koyarwarsa :ya zo da daidaito tsakanin dukkan hAlitta da ‘yanuwantaka da rangwame na gaba daya ga wanda ya shiga musulunci, sannan ya kafa shari’a madaukakiya da dokoki na adalci da ya karbo daga wajan Allah su kuma musulmi suka karba daga gare shi.

Mu’ujizozinsa :mu’ujizarsa madauwamiya ita ce alkur’ani amma wadanda suka faru a farkon musulunci suna da yawa ba sa kuma kirguwa.

Kiransa :ya kira mutane zuwa ga tauhidi a makka a boye shekara uku ya kuma kira su a bayyane shekara goma.

Hijirarsa :ya yi hijira daga Makka zuwa Madina a farkon watan rabiul auwal bayan shekara 13 daga aikensa, wannan ya faru ne sakamakon cutarwa daga kafirai gare shi da kuma ga sahabbansa.

Yakokinsa :Allah ya yi wa manzo izinin yakar mushirikai da kafirai da munafukai, sai ya yi dauki ba dadi da su a wurare da yawa da mafi girmansu sune :Badar- Uhud- Al-khandak(ahzab)- Khaibar- Hunaini.

Matansa:Khadija ‘yar khuwailid  ita ce matarsa ta farko, amma sauran sune :Saudatu ‘yar Zami’a da Aisha ‘yar Abubakar da Gaziyya ‘yar Dudan (Ummu sharik) da Hafsa yarUmar da Ramla ‘yar Abu sufyan (ummu habibia) da Ummu Salama ‘yar Abu Umayya da Zainab ‘yar Jahash da Zainab ‘yar Huzaima da Maimuna “yar Al-haris da Juwairiyya ‘yar Al-haris da Safiyya ‘yar Huyayyi dan Akhdabl.

‘ya’yansa :su ne 1- Abdullah 2-Al-kasim 3-Ibrahim     4-Fadima (AS) a wani kaulin da Zainab da Rukayya da Ummu Kulsum.

Ammominsa :su tara ne su ne ‘ya’yanAbdulmudallib :Al-haris da Zubair da Abu Dalib da Hamza da Al-Gaidak da Dirar Al-mukawwam da Abulahab da Abbas.

Ammominsa mata :su shida ne daga iyaye mata daban daban su ne :Amima da Ummu hakima da Barra da Atika da Safiyya da Arwa.

Wasiyyansa goma sha biyu ne su ne:Amirulmuminina Ali  (AS)  da Al-hasan dan Ali  da Al-husaini dan Ali  da Aliyyu  dan Husaini  da Muhammad  dan Ali  da Ja’afar dan Muhammad  da Musa dan Ja’afar da Ali dan musa da Muhammad dan Ali da Ali dan Muhammad da alhasan dan Ali da Hujjat dan Al-hasan Al-mahadi (Allah  ya gaggauta bayyanarsa).

Mai tsaron kofarsa :Anas dan Malik

Mawakansa:Hassan  dansabita da Abdullahi dan Rawahata da ka’abu dan malik.

Mai kiran sallarsa:Bilal al-habashi da Dan ibn ummu maktum da sa’ad al-kirdi

Hatimin zobensa:(Muhammadur rasulullah).

Tsayin rayuwarsa :shekaru 63.

Tsayin lokacin annabtarsa :shekaru 23.

Tarihin wafatinsa:28 safar11 H.

Wajan da ya yi wafati:madina.

Inda aka binne shi:madina a masallaci madaukaki mai alfarma.