Home Page
 Tarihin rayuwarsa
   Akidojin Shi'a
   Littafansa
   Fatawoyi
   Sakonni
   Darussa
   Littafan dansa
   Dakin karatu
   Hotuna


Affiliate Websites
Affiliate Websites

   E-Mail Listing:


 

Sakon Ayatullahi Alnkarani dangane da shahadar Imam Askari da kuma  wasu malamai a Najaf

  Da sunan Allah mai rahma.

  Ina si in yi nuni zuwa ga abubuwa guda biyu a nan, na farko shi ne, gobe  Laraba wanda zai zama ran ace ta tunawa da   kama wasu manyan malamai wadan da Sadam ya ba da umurni a ka kama  su wanda muta ne suna tsammanin cewa an kaisu ne gidan kurku,duk da cewa ga dukkan alamu  azzalumin nan mai busassar zuciya wato Sadam   ya gama da su ne,duk da cewa akwai wani tsammanin cewa wasu daga cikinsu wadan da suke matasa ne 'yan uwansu na sa ran cewa za'a sakosu su koma zuwa ga gidajensu.

      Bayan wannan abin da ya faru na Iraki kwanannan wato na korar sadam daga mulki sai ya  bayyana cewa bayan an je gidajen kurkuku sai a ka samu cewa ai lallai sadam duk ya gama da malaman nan wadan da yawansu ya kai mutum dari da hamsin. Da yawa daga cikinsu Iraniyawa ne wadansu kuma daga cikinsu ma sun kai  matsayin marja'iyya.Sannan kuma akwai da yawa daga cikinsu daga iyalin  wani marja'i guda daya ne aka kama. Wasu daga cikinsu sun kasance abokaina ne, shekarun wadan nan mutane kuwa maban-banta ne wanda ya fara daga 40-90.Daga karshe ya tabbata wannan azzalumi mashayin jinin bayin Allah duk ya gama da su.

   Dangane da ilimimsu kuwa ni da kaina na san wasu daga cikinsu wadan da suke lallai manyan malamai ne kuma marubuta amma duk an yi asararsu.wanda daga cikin rubuce-rubucensu anan wajen karatunmu mun anfana da bahsinsu a cikin babin  hajj.

  Don haka gobe Laraba domin tunawa da kuma girmama matsayin iliminsu an ba da hutu  a duk cibiyoyin nazarin addinin musulunci(hauza) dake cikin kasar nan da sauran kasashe, domin wannan al'amari maigirma.

   Dagutu zamaninmu ma haka ya so ya yi anan iran ya gama da dukkan malamai da cibiyoyin nazarin addini, sai Allah bai ba shi iko ba, sakamakon haka ma sai Imam khomaini (r.a) tare da taimakon Allah ya kawar da shi daga cikin wannan al'umma.

    Don haka dagutu duk inda yake abu guda ne, Dagutun Iraki ma haka ya so ya gama da hauza a cikin iraki har ya zuwa karshen mulkinsa, kuma lallai ya yi mana babban gurbi.Sai dai  kaico yanzu mene ne sakamakonsa muna iya cewa Allah ya fara kama shi kafin zuwa ga azabar lahira wadda itace mafi tsanani, wato  sakamakon kisan da zaluncin da ya yi wa malamai bayin Allah a cikin iraki da yakin da janyo wa mutanen iran da  na irakin baki daya asarar rayuka da dukiya. Ya Allah kafin azabar lahira ka azabtar da shi sakamakon zaluncinsa.

   Saboda haka dangane da wannan ne gobe dukkan makarantu hutu ne saboda da girmama wannan rana.

   Amma abu na biyu da zanyi nuni zuwa gare shi, shi ne, ranar Asabar ranar takwas ga wata  ne wanda ya yi dai dai da shadar Imam Askari a.s wanda  kuma shi ne mahaifin Imamul hujja a.s, don haka ne kasuwanni ma gobe hutu ne. Saboda haka dole ne mu kiyaye wannan ma'ana ta shahadar Imam mu kuma girmama wannan hakikakanin girmamawa, saboda haka ranar  Asabar babu karatu hutu ne, Idan Allah T.A ya bam u iko zamu cigaba da karatu ranar Lahadi.

   Wassalam.