Home Page
 Tarihin rayuwarsa
   Akidojin Shi'a
   Littafansa
   Fatawoyi
   Sakonni
   Darussa
   Littafan dansa
   Dakin karatu
   Hotuna


Affiliate Websites
Affiliate Websites

   E-Mail Listing:


 

Sakon Ayatullahi Lankarani Dangane da sha biyar ga watan sha'aban 1423.

Bayan godiya ga Allah da satali ga manzon tsira da iyalansa,sha biyar ga sha'ban ranar haihuwar haske ce wanda shi ne hujjar Allah ta karshe a bayn kasa, ranar da ta zama digon farko na tabbatr da adalci a bayan kasa,ranar Allah madaukaki ya baiwa bayinsa babbar ni'ima ya bas u mai ceto wato Imam Mahdi a.s.

Duk da cigaban dan Adam a rauwa wadda bata da iya kuma kullun sai karuwa take,ta ydda dan Adam bai takita ba kawai a bias kasa hae zuwa bias duniyar wata ya kai, dan Adam ya samu cin nasarori da dam ta wannan fanni,amma kaico duk yadda dan Adam ya samu Karin cigaba ta fuskar kimiyya da fasaha kuma yakan kara nisa day an adamtada ya kuma kara kaifin zalunci da nisa da hankalin da Allah ya ba shi don rayuwar da ta dace.

 A yau al'ummar duniya tana ganin yadda zalunci manyan kasashen duniya  wadan da suke kokarin zama ba wanda zai iya shiga a gabansu.Tare da labewa da yaki da ta'addanci suna zaluntar al'umma masu raini marasa karfi, sannan suna tsorata duniya da karfin da sule da shi,don haka ne dunoya take cike da bukatar maiceto daga Allah domin ya cece su daga wannan bakin zalunci ya kafa hukuma ta Allah ta yadda adalci zai game duniya baki daya.

 Dan Adam ya nuna cewa duk da cigaban day a samu amma ya kasa tabbatar da dalci a cikin al'umma,haka ma kungiyoyin kare hakkin dan Adam sun kasa kwato hakkin masu rauni daga azzalumai, a hakikanin gaskiya ma sune suka kafa su.Shinkasance mutum ya cigaba da shan wahalhaloli irin wadan nan har abada?Shin Allah ba wata hanaya da tanada ta yadda zai cececi dan adam daga wannan zalunci, ko kuwa Allah ya kasa ne? muna neman tsari daga wannan.Lallai ba haka ban e wannan ya saba wa hadafin halittar dan Adam.Sannan alkawalin akan samun nasarar addinin Allah akan sauran addininai ya saba wa hakan,hikimar Allah tana nuni da cewa lallai dole ne a samu wani wanda yake shi ne mafi sani da adaukaka a cikin mutane ta yadda zai dauki wannan nauyi na tabbatar adalci a bayan kasa.A yau dukkan shi'a suna cike da gurin tabbatar gwamnain adalvci ta hanya Imam mahdi a.s ta yada adalcin Allah zai tabbata kuma zalun yak au a doron kasa. Duk da yake a shekarun nan na karshe an samu wannan kulawa dangane da Imam mahdi a.s. daga sauran musulmin duniya.Don haka ne mutane suka cigaba da bayyanar alamomin bayyanar Imam da yadda hukumarsa zata kasance.Don haka ta bangarena ina gabatar da godiyata ta musamma zuwa ga wadan da suke irin wannan hidima.Sannan ina kira zuwa gare su da dage kwarai da gasket wajen bayyana wannan hakika tare da kula da samo bayanai daga littafai masu inganci.Tare da godiyar Allah muna da littafai da dama a wannan fage,wadan da ba mu da shakku akan su.Muna da manayan ingantattun littafai da suke bayani dangane da Imam a.s, wadan da suka hada tun daga haihuwarsa hae ya zuwa hukumarsa, saboda haka masu bukata kuma masu zuciya tsarkakka suna iya samunsu a ko,ina.

Ina kira ga dukkan musulmi masu himma da dage wajen fadada wannan tunani a duk inda suke ta yadda al'umma zasu samu ilimi da kuma soyayya ga wannan Imam a.s.Ta yadda Imam zai tabbatar da adalci ya kuma kawar da zalunci a doron kasa.

A yau aiki kowane musulmi shi ne,ya yi imani da cewa dukkan ni'imomi da albakatu da muke samu dukkansu suna zuwa ne daga wannan shugaban adalci Imam Mahdi a.s.Fadar Allah madaukaki"Ba don hujja ba  da duniya ta ruguje da abin da ke cikinta".Don haka dukkan albarku suna zuwa ne daga gare shi, saaboda haka abin day a hau kanmu don godiya ga wannan ni'imomi shi ne, mu yi kokari birane da kauyukla mu raya wanna akida da farkar da mutane daga barcin gafala da suka shiga da koma wa zuwa ga Allah, ta hanyar gabatar da taruka don bahsi dangane da Imam a.s. Don haka ina kra ga shuagabanni da su yi kokar su rika shirya taruka a cikn gida da waje don raya wannan al'amari da yardarm Ubangiji zai amfanar cikin sauri ta yadda mutane zasu samu masaniya dangane da Imam da kuma hukumarsa.

   Ina rokon Allah madaukaki da kawar da dukkan abin zai hana bayyar sa a.s.Ta yadda zai 'yantar da al'ummar musulmi musamman sha'a daga wannan bakin zalunci da tabbatar da  hukumar adalci a bayan kasa insha Allah ta a'la.

 Muhammad fadhil lankarani
Sha'ban 1423.