Home Page
 Tarihin rayuwarsa
   Akidojin Shi'a
   Littafansa
   Fatawoyi
   Sakonni
   Darussa
   Littafan dansa
   Dakin karatu
   Hotuna


Affiliate Websites
Affiliate Websites

   E-Mail Listing:


 

Baya kanu Gaba

Kasa

Mas'ala ta 187:Kasa tana tsarkake kafa ko takalmi mai najasa tare da sharudda biyar:

Na daya:kasar ta zama mai tsarki.

Na biyu:Kasar ta zama busassa.

Na uku:Idan tafin kafa ko takalmin da ya samu najasa ta hanayar tafiya a bisa kasar ne ko kuma ta hanayar  goga kafar ko takalmi  bisa kasa najasar ta gushe.

Na hudu:Kasar dole ne ta zama turbaya, yashi ko dutsi, amma idan ya zama bisa  wani abu kamar shinfida ne aka yi tafiya ko aka goge najasar, ba ta tsarkaka.

Na biyar:Sanana ya zamana ta hanyar tafiya ne aka samu najasar,amma idan ta wata hanya aka samu najasar; tsarkake ta ta hanyar tafiya bisa kasa yana da matsala.

Mas'ala ta 188:Takalmi ko tafin kafar day a samu najasa ta hanayar tafiya bisa kasa, ba ya zama mai tsarki ta hanyar bisa tile ko kwalta ko bisa daben da aka yi shi da katako.

Mas'ala ta 189:Wajen tsarkake takalmi ko tafin kafar day a samu najasa, dole a yi tafiya bisa kasa a kalla taki goma sha biayar koda kuwa najasar ta gushe kafin tako gama sha biyar din.

Mas'ala ta 190:Bad le ban e kafa ko takalmin day a samu najasar su zama masu lema, koda ta bushe sakamakon tafiya idan ta gushe sun tsarkaka.

Mas'ala ta 191:Bayan tafiyar da ka yi da takalmi ko tafin kafa ta yadda suka tsarkaka gefensu ma ya tsarkaka.

Mas'ala ta 192:Wanda yake tafiya da wannu da guyawunsa(gurgu)idan tafin hannunsa ko guyawunsa suka samu najasa, tsarkake su ta hanayar tafiya yana da matsala.Haka nan ma kasan sanda ko kafar da ake yi ta katako ko ta roba, takalmin garagu masu tafiya da hannun da guyawu, tayar mota ko keke, da dai makamantansu. ba a tsarkake su ta hanayar tafiya idan suka samu najasa.

Mas'ala ta 193:Idan sakamkon tafiya aka gusar da najasa akan takalmi ko tafin kafa, amma said dan wani abu daga najasar ya ragu amma ba iya ganinsa, abin day a fi shi ne a yi koakri a gusar da shi duka,amma ragowar  launi ko wari babu matsala.

Mas'ala ta194:Bangaren kafa ko takalmi dab a su isa bisa kasa yayin tafiya sakamkon yafiya ba su tsarkaka.Haka nan tsarkake kasan safa ta hanyar tafiya ba  yana da matsala,amma idan kasan safar na fata ne yana tsarkaka sakamakon tafiya.

Rana

Mas'ala ta 195:Rana tana tsarkake kasa da gini da duk abin da baya daukuwa kamar koaf ko taga da dai makamantansu,haka nan ma kusar da ke jikin bango ana lissafa ta ne bangaren ginin, idan suka samu najasa rana tana tsarkake su tare da sharudda guda shida.

Na daya:Abu mai najasar ya zama mai leman e ranar ta busar da shi,don haka idan ya kasance busasshe yayin da rana take bugunsa bay a zama mai tsarki.

Na biyu:A kawar ainahin najasar akan abin kafin ranar na buge shi.

Na uku:Kada wani abu yak are shi daga  ranar ya zama bugub ranar ne ya busar da shi, amma idan ya zama kamar labule ko giza-giza marar kauri sukan dan kare babu matsala.

Na hudu:Ya zamana ranar ce kawai ta busar da abin, don haka idan abin ya bushe ne sakamakon iska tsarkinsa  yana da matsala,amma idan isakan kadan ta yadda ba za a ce shi ya busar da abin ba, ba matsala.

Na  biyar:Idan kasa ko ginin da ya samu najasa ya zamana najasar ta shiga cikinsa, idan ranar a loakci guda ta busar da shi duka,ciki da bayansa suna tsarkaka.Amma idan a lokaci na farko kawai ranar ta busar da bayansa ne amma cikinsa bai bushe ba, kawai bayansa ne zai zama mai tsarki.

Na shida:kada ya zama tsakanin cikin gini ko karkashin kasar da ta samu najasa, akwai abin ya kare rana ta isa zuwa gare shi.

Mas'ala ta 196:Rana tana tarkake tabarmar da ta samu najasa, haka nan itaciya ko ciyawar da suka sami najasa suna tsarkaka yayin da rana ta busar da su, da sharadin ya zama babu ainahin najasar.

Mas'ala ta 197:Idan rana ta bugi kasar da take da najasa, sai mutum ya yi shakka akan cewa shin lokacin da rana ta bugi kasar nan, shin ta kasance mai lema ko kuwa a'a, sannan idan tana da lema shin ranar ce ta busar da ita ko kuwa, anan hukuncinsa shi ne har yanzu akwai najasar.

Mas'ala ta198: idan rana ta bugi wani bangare na bango, bangaren da ranar ba ta buga ba, bai tsarkaka ba.Amma idan bangon ya kasance marar kauri ta yadda ranar ta  iya busar da shi ba matsala, shima ya tsarkaka.

Canzawar najasa

Mas'ala ta 199:Idan abin da yake da najasa ya canza zuwa wani abu daban ya zma mai tsarki.kamar katako mai najasa idan aka kona shi tokarsa  mai tsarki ce.ko kuma saka kare cikin kogin gishiri idan ya zama gishiri ya zma mai tsarki.Amma idan abu bai canza ba zuw wanidaban bay a tsaekaka,kamar idan alama mai najasa ta koma gari har yanzu tana nan mai najasarta.

Mas'ala ta 200:Biutar kasa wadda aka yi da kasa mai najasa ita ma najsa ce.Don haka  ya kamata a kaurace wa gawayin da aka samu da ice mai najasa.

Mas'ala ta 201:Abu mai najasa da ake shakku akan shin ya koma wani daban ko kuwa yana nan halinsa na da, najasa ne.  

Baya kanu Gaba