Home Page
 Tarihin rayuwarsa
   Akidojin Shi'a
   Littafansa
   Fatawoyi
   Sakonni
   Darussa
   Littafan dansa
   Dakin karatu
   Hotuna


Affiliate Websites
Affiliate Websites

   E-Mail Listing:


 

Baya kanu Gaba

Kawar da ainahin najasa

Mas'ala ta 220:Idan jikin wata dabba ya samu najasa kamar jini ko kashi da zarar wannan najar ta kau daga jikin dabar, ta tsarkaka ba sai an wanke jikinta ba.Haka nan idan  abin da ke cikin jikin mutum ya samu najasa sai ta kau ba sai an wanke ba, misali kamar mutum sakamakon jinni day a fito daga dasashinsa sai bakinsa ya samu jinni idan wannan jinni ya bace tare da ywu ba sai mutum ya wanke bakinsa ba.

Mas'ala ta 221:Haka idan abinci ya yi saura jikin hakorin mutum sai jini daga cikin bakin mutum ya taba abicin bayan gushewar jinin mai tsarki ne, hakoran da ake saw a mutum na roba ko makamancinsu idan sun taba jinni cikin baki ba sai an wanke sub a.

Mas'ala ta 222: A wurin da mutum bai sani ba shin aa lissafa shi ne cikin abin yake cikin jik ko kuwa an lissafa shi ne wajen jiki, idan wurin ya taba najasa ba dole ban e ya wanke shi, da zarar najasar ta kau ya zama mai tsarki, sai dai abin day a fi shi ne ya wanke din.

Mas'ala ta 223:Idan kura mai najasa ta taba jikin mutum ko tufafi da makamantansu, sannan kuma duka biyun bas u da lema wait kura da kuma bain da kurar ta taba, ba bu wat matsala, amma idan duka ko daya daga ciki yana da lema dole ne a wamke wajen da kurar ta taba.

Tsarkake dabbar da take cin najasa:

Mas'ala ta 224:Kashi ko fitsarin dabbar da ke cin najasa kamar kashi ko fitsarin mutum  kashi da fitsarinta najasa ne.Idan ana so a tsarkake wannan dabbar dole a tsareta zuwa wani lakci tana cin abinci mai tsarki ta yadda  ba za a ce mata mai cin najasa ba.Idan rakumi ne kwana arba'in,sanuwa kwana ashirin, tunkiya da akuya kwana goma,agwagwa kwan biyar kaza kuwa kwana uku,wannan shi ne hanyar tsarkake irin wadan nan dabbobin da suke cin najasa.

Fakuwar musulmi:

Mas'ala ta 225:idan jikin musulmi ko tufafinsa ko wani abu da yake da shi ya zama najasa, bayan faku daga gare mu zuwa wani lokaci, sai ya sake dawo inda muke, zamu yi wa jikinsa da duk abin da yake da shi hukuncin tsarki tare da sharudda kamar haka:

1-musan cewa jiki da tufafi ko kaynsa sun kasance masu najasa,

2-Sannan amfani da wadan ana kayan dole sai suna da ysarki.

3-Sannan muna kyautata zaton cewa ya tsarkake su.

Mas'ala ta 226:idan tufafi ko ko wani abin amfanin mmusulmi suka samu najasa, sai wannan musulmin ya faku, idan mutum ya yi tsammanin cewa lallai wannan mutum ya tsarkake kayansa, ba dole ban e mutum ya kauracewa wadan nan kayanmko ya wanke su, tare da sharadin cewa mutum ya san cewa wadan nan abubuwa sun kasance ma su najasa kuma wanda yake da su baligi ne kuma wanda ba ya wasa tsakkake kayansa, sannnan kuma sharadi ne amfani da kayan sai da tsarki.

Mas'la ta 227:Idan mutum ya samu yakini da kansa akan cewa abin da yaksance mai najasa ne an tsarkake shi ko kuma adalai guda biyu suka ba shi labarin tsarkake abin hukunsa mai tsarki ne, ko kuma idan musulmi ya tsarke abu koda mutum yana zaton cewa akwai yiwuwar cewa ba a tsarkake shi da kyau ba, hukuncinsa mai tsarki ne sai idan ya samu ayakini akan cewa bai tsakaka ba.

Mas'ala ta 228:Idan aka wakilta mutum akan ya tsarkake wani tufafi ko wani abu,sai ya ce ya tsarkake abin to hukuncin abin maitsarki ne.

Mas'ala ta 229:Idan mutum yana da wani9 hali ta yadda ya kanyi kokwanto akan cewa shin wannan abin mai najasa ya tsarkaka ko kuwa, idan ya yi kamar yadda saura mutane suke yi, ba dole ban e sai shi kansa ya samu yakini akantsarkin abin.

Baya kanu Gaba