Home Page
 Tarihin rayuwarsa
   Akidojin Shi'a
   Littafansa
   Fatawoyi
   Sakonni
   Darussa
   Littafan dansa
   Dakin karatu
   Hotuna


Affiliate Websites
Affiliate Websites

   E-Mail Listing:


 

Baya kanu Gaba

Sharuddan ingancin alwalla

sharadi na farko: dole ne ruwan da za'a yi alwalla ya zama mai tsarki.

Sharadi na biyu:dole ruwan alwalla ya zama marar gauraye.

Mas'ala ta 270:Alwalla da ruwa marar tsarki ko mai gauraye ta baci.Idan mutum ba ya da sani a kan tsarki ko rashin gaurayen ruwa kjo kuma ya manta,to dole ne ya sake alwallar da ya yi da ruwan haka idan ya yi salla da wannan alwallar ya sake sallar.

Mas'ala ta 271:Idan mutum bai samu wani ruwa ba da zai yi alwalla sai ruwan da yake da gauraye da wani abu, sannan ga shi lokaci ya kure wanda zai iya samun wani ruwan, anan sai ya yi taimama ya yi salla,amma idan akwai lokaci sai ya yi hakuri har sai ya samu wanda ba wannan ba.

Sharadi na uku: dole ruwan alwalla ya zma na halas.

Mas'ala ta 272:Alwalla da ruwan da yake na kwace ko kuma mutum yasan cewa mai wannan ruwan bai yarda ayi masa alwalla da ruwa ba, wannan alwallar haramun ce kuma ta baci.Amma idan mutum ya san cewa mai wannan ruwan da ya yarda a yi alwalla da ruwansa amma yanzu  mutum yana shakka akan cewa shin yanzu ya maince ko abi aminta a yi alwalla da ruwan na sa ba, anan idan mutum ya yi alwalla da ruwan alwallarsa ta ta yi kuma babu wani laifi.Haka nan idan lokacin mutum yake alwalla sai ruwan alwallar ya zuba a wani wuri wanda ya ke na kwace, shi ma alwallarsa ta inganta.

Mas'ala ta 273:Idan mutum ya yi alwalla da ruwan wata makranta wadda yake zaton cewa shin wannan ruwan ya takaita ne kawai ga 'yan makarantar ko kuwa,amma kuma ya san cewa mutane suna yin alwalla a wanna wurin wanda yake nuna cewa, bai takaita ba kawai ga 'yanmakarantar, to anan shima alwallarsa ta inganta.

Mas'ala ta 274:wanda ba ya so aya yi salla a wani masalaci amma sai yake shakka akwan cewa shin ruwan wanna masallacin ya takaita ne kawai ga masu salla wanna masallaci ko kuwa? a nan ba zai ya yin alwalla da wannan ruwan ba.Amma idan ya kasance sauran alumma koda ba nan zasu yi salla ba, su kan yi alwalla a wajen ta yadda yake nuni da izinin yin hakan. to ana babu laifi nutun ya yi alwalla da ruwan wannan masallaci.

Mas'ala ta 275:Yin alwalla da ruwan gidan baki da hotel da makamantansu ga wanda yake shi ba wurin yake ba,tana inganta ne kawai idan dama ya kasance wasu mutane wadan da ba nan suke  ba sukan yi amfani da wannan ruwa wajen yin alwalla.

Mas'ala ta 276:Yin alwalla ta ruwa manyan koramu idan mutum ya san cewa wanda yake da su bai yi hani akan yin alwalla da su ba, to anan mutum yana iya yin alwalla kuma ta inganta,Amma idan mutum ya san cewa wanda ke da wannan korama ya yi hani a a kan yin alwalla da ruwan wannan korama,ana bai halitta ba mutum ya yi alwalla da ruwan koramar.

mas'a la ta 277:Idan mutum bai san cewa wannan ruwan na kwace ne ba, ko kuma ya manta, sai ya yi alwalla da ruwan alwallarsa ta inganta.

Sharadi na hudu:dole ne ya zama wurin da za.a zuba ruwa a ciki a yi alwalla na halas ne.

Sharadi na biyar:Kada ya zama abin da ka zuba ruwan alwalla zinari ko azurfa.

Mas'ala ta 278:Idan ruwan lawalla ya kasance a cikin abin da yake na kwace ne,sanna babu wani wurin da zai zuba ruwan, anan mutum sai ya yi taimama.Saboda haka idan mutum ya yi alwalla da wadan nan ruwan alallarsa ta baci.Amma idan mutum yana da ruwa kuma na halas,haka nana ma idan ya yi lawallar a cikin kwano wanda yake na kwace,idan ya yi alwallar irtimas,ko kuma ya dauki wannan kwanon ku butar ya zuba ruwan a fuskarsa ko hannayensa, alwallarsa ta baci.Amma idan ya debo ruwan da tafin hannunsa ya zuba a fuskarsa da hannayensa, alwallarsa ta inganta,duk da cewa yin amfani da ya yi da buatr da take ta kwace haramun ne.Haka nan alwalla a cikin butar zinari ko azurfa kamar yadda muka fada a wannan.

Mas'ala ta 2789:Idan ya kasance a cikin ruwan lawalla akwai tubali ko dutse na kwace idan mutum ya yi alwalla da ruwan ta inganta.

Mas'la ta 280:Idan aka yi wani wuri da ke zuba ruwa ko wat korama a cikin filin kabarin wani daya daga jikin jikokin Annabi s.a.w.a Sannan mutum ba ya da masaniya kan cewa shin an kebance wannan wuri ne saboda wasu mutane na musamman ko kuwa,idan mutum ya yi alwalla da wannan ruwan ta inganta.

Sharadi na shida:Dole ne ya zamana wuren da ake wankewa ko shafa su kasance masu tsarki.

Mas'ala ta 281:Idan bayan an gama alwalla sai wani wuri ya samu najasa, alwallar ta inganta sai dai kawai a wanke wurin da ya samu najasar kafin a yi salla.

Mas'ala ta 282:IDan wani wuri daga cikin jikin mutum wanda ba wurin da ake alwalla ba ya ka sance mai najasa alwalla ta inaganta.Amma idan ya kasance wurin kashi ko fitsari ne ba a tsarkake ba, to ya kamata a tsarkake sannan a yi alwalla.

Mas'ala ta 283:Idan ya kasance daya daga cikin gabban alwalla mai najasa, sai bayan alwalla mutum ya yi shakka a kan cewa shin ya tsarkake wannan wurin kafin alwalla ko a'a, haka nan idan yana shakku a kan cewa ba shi da masaniya lokacin da yake alwalla shin ya wanke ko kuwa bai wanke ba, anan alwallarsa ta baci, Amma idan ya san cewa  yana da masaniya lokacin da yake alwalla ko yana shakku akan hakan alwallarsa ta inganta.Duk da haka nan dole ne a wanke inda ya samu najasar kafin a yi salla.

Mas'ala ta 284:Idan ya kasance a bisa fuska ko hannaye akwai rauni ta yadda jini baya fitowa daga daurin da a ka yi, sannan ruwa ba zai cutar ba a wurin, annan dole ne sanya wurin a cikin ruwan kur ko ruwa mai gudu sannan a danna wurin ta yadda jinin da ke jikin dauri ya fita sannan a yi alwalla ta irtimas kamar yadda muka nuna yadda a ke yi   a baya.

Sharadi na bakwai:Dole ne ya zama akwai lokacin da zai isa a yi alwalla sannan a yi salla.

Mas'ala ta 285:Idan ya kasance sakamakon kurewar lokaci yin alwalla zai janyo a yi sallar bayan lokaci ko kuma wani bangare daga cikin sallar, to anan sai mutum ya yi taimama don ya yi sallar cikin lokaci,ammam idan ya zamana loakcin da za'a dauka wajen yin taimama duk daya ne da yin alwallar, to anan sai ya yi alwallar.

Mas'ala ta 286:Wanda ya kasance a cikin kurarren lokaci wanda ya kama ya yi taimama ne, idan ya yi alwalla, alwallar ta inganta don yin wannan sallar da wani aiki daban ma wanda yake bukatar alwalla.

Sharadi na takwas:Ya zama an yi alwala neater da  niyyar kusanci ga Allah T.A. sabooda haka idan mutum ya yi alwalla da niyyar sanyaya jikinsa ko wata manufa daban alwallarsa  ta ba ci.

Mas'ala ta 287:Ba dole ba ne mutum ya yi niyya da bakinsa, kawai idan mutum ya kudurta a cikin zuciyarsa ya wadatar, sai dai dole ne mutum ya zamana hankalinsa yana nan wajen alwallar har ya gama, ta yadda idan da za'a tambaye shi me yake yi zai ce alwalla nake yi.

Sharadi na tara: Dole ne a gabatar da alwalla a jere kamar yada aka yi bayani.Wato farko a wanke fuska sannan hannun dama sannan na hagu,sannan sai a shafi kai da kafafu da lemar hannu, sannan abin da ya fi dacewa shi ne, a fara shafar kafar hagu sannan ta dama.Idan mutum bai bi jerin da aka fada ba alwallarsa ta baci.

Sharadi na goma:Dole a aiwatar da ayyukan alwalla ba tare da tsawaita lokaci ba a tsakann juna.

Mas'ala ta 288:Idan ya zamana akwai tsawon lokaci tsakanin ayyukan alwalla ta yadda kafin ya wanke ko ya shafi wani wuri wanda ya riga ya wanke ya bushe alwaallarsa ta baci.Amma idan ya kasance kawai wanda ya wanke ba tare da tsakani ba ne ya bushe, misali kamar hannun dama ne ya bushe kafin ya wanke na hagu,amma fuska tana da lema anan abin da ya fi shi ne, ya sake alwallar tun daga farko.

Mas'la ta 289:Idan ya zamana mutum ya aiwatar da ayyuakan alwalla ba tare da bata lokaci ba, amma saboda da tsananin zafi ya sanya wasu wuraren sun bushe kafin ya gama, alwallarsa ta inganta.

Mas'ala ta 290:Babu laifi a yi tafiya yayin alwalla, idan ya zama bayan mutum ya wanke fuska da hannu sai ya dan taka sannan sai ya shafi kai da kafa, alwallarsa ta inganta.

Sharadi na goma sha daya:Dole ne mutum ya aiwatar da ayyukan alwalla da kansa, idan da wani zai yi masa alwalla ko ya ytaimaka masa wajen yin alwalla, alwallarsa ta ba ci.

Mas'ala ta 291:Wanda ba zai iya alwalla ba da kansa ya halarta ya nemi wani wanda zai iya taimaka masa.Sannan idan ya nemi lada idan yana da hali dole ya ba shi,amma abin da ya fi dacewa shi ne mutum da kansa wanda wanda zai taimaka masa wajen alwallar su yi niyya ba ki daya. Sannan idan yana iyawa dole ne ya yi shafa da kansa, idan kuwa bay a iyawa da kansa sai wakilin nasa ya kama hannunsa ya yi masa shafar,Idan kuwa wannan ma ba zai yiwu ba, to sai ya yi masa shafar amma da lemar hannunsa,.Sannan abin da  ya fi dacewa a cikin wannan hali bayan alwalla a hada da taimama.

Mas'ala ta 292:Duk abin da  mutum yake iya aiwatarwa da kansa bai kamata ba mutum ya nemi taimako wajen aikata wannan din.

Sharadi na goma sha biyu:Ya zama ba wani abu da ya hana mutum yin amfani da ruwa.

Mas'ala ta 293:Wanda ya ke jin tsoron idan ya yi amfani da ruwa wajen yin alwalla zai yi rashin lafiya, ko kuma idan ya yi amfani da ruwan zai bukaci ruwa domin sha,anan idan ya yi alwalla da ruwan alwallarsa ta ba ci.Amma bai san cewa ba idan ya yi mafani da ruwa zai cutar da shi, sai bayan ya yi ya fahimci cewa zai cutar da shi anan alwallarsa ta inganta.Duk da cewa kada ya yi salla da wannan alwallar shi ya fi.Haka nan idan ya riga ya yi salla da wannan alwallar abin da  ya fi shi ne ya sake wannan sallar.

Mas'ala ta 294: Idan  ya kasance ruwan da aka yi amfani da shi wajen alwalla kadan  ne amma ya wadatar wajen ingancin alwalla, babu matsala kasancewarsa kadan ne.Sannan yin amfani da wanda ya fi haka yana iya cutarwa,wajibi ne a yi amfani da wannan din.

Sharadi na goma sha uku:Kada wani abu  ya hana ruwa isa zuwa bisa gabban alwalla.

Mas'ala ta 295:Idan mutum ya san cewa akwai wani abu da ya  like bisa fatarsa ta gabar alwalla,amma yana shakka a kan cewa shin yana haka ruwa isa zuwa bisa fata ko a'a, anan dole ne ya kawar da abin, ya isar da  ruwa bisa fatar.

Mas'ala ta 296: Idan ya kasance akwai maiko karklashin farce, babu matsala wajen yi alwalla,amma idan ya yanke farcen dole ne ya kawar da wannan maiko wanda zai hana ruwa isa bisa fata kafin ya yi alwallar.Haka nan idan ya kasance farce yana da tsawo wato ya wuce misali,idan wannan maikon yana karkashin wannan farcen wanda ya wuce dan yatsa dole ne ya gusar da wannan maikon kafin ya yi alwalla.

Mas'ala ta 297:Idan ya kaance a bisa fuska ko wani wuri da ake alwalla akwai wani bololo sakamakon konewa ko wani abu wankewa ko shafar  samansa yayin alwalla ya wadatar.haka nan idan wani wuri ya yi rami ba dole ba ne mutum ya sanya ruwa ya shiga har can ciki.Saboda haka idan wani bangare fata ta cire amma dayan bangarenta bai cire ba, ba dole ba ne mutum ya shigar da ruwa karkashin fatar da ba ta cire ba,haka nan idan fata ta tashi jikin mutum ta yadda wani lokaci takan rabu da jikin mutum ya kamata a yanke ta ko kuma a isar da ruwa karkashinta yayin alwalla.

Mas'ala ta 298:Idan mutum yana shakka akn cewa shin wani abi ay like jikin gabar alwalla ko kuwa, ta yadda sauran mutane ma suna wannan tsammanin.misali kamar mutumm ya yi aikin kasa sai mutum yana shakka akan cewa shin wannan kasar ta like masa ko kuwa,anan dole ne mutum ya bincika ta yadda zai tabbatar da cewa akwai ko babu.

Mas'ala ta 299:Wurin da dole ne a wanke sa ko shafe shi yayin alwalla idan ya zamana akwai wani maiko wanda ba zai hana ruwa ba isa bisa fatar, ba dole ban e sai an gusar da wannan maikon.Haka nan idan utum y agama shafa farar kasa sai ya ga wani fari a jikinsa amma ba ya hana ruwa isa bisa fatarsa, yin alwalla da wannan ba wani laifi,amma idan mutum yana shakka akan cewa shin zai iya hana ruwa isa ko kuwa, anan dole ne mutum ya gusar da shi kafin alwalla.

Mas'ala ta 300:Idan mutum kafin ya yi alwalla ya san cewa akwai wani abu wanda zai iya hana ruwa isa bisa gabban alwalla,sai ya yi bayan alwalla  yake shakka a kan cewa shin lokacin alwalla ruwa ya isa bisa wannan gabar ko bai isa ba, sannan kuma ya na tsammanin cewa lokacin alwallar hankalinsa yana nan, alwallarsa ta inganta.

.Mas’ala ta 301:Idan ya kasance akwai wani abu da zai iya hana ruwa isa zuwa ga gabban alwalla ta yadda wani lokaci yana isa wani loakaci ba ya isa, anan idan mutum ya gama alwalla sai ya yi shakka akan cewa shin ruwa ya isa bisa fatarsa ko kuwa bai isa ba,Sannan kuma ya san cewa lokacin da yake alwallar hankalinsa ba ya nan  a kan cewa shin ruwa ya isa ko bai isa ba, anan abin da ya fi shi ne ya sake alwallar.

Mas’ala ta 302:Idan mutumm bayan ya gama alwalla sai ya ga wani abu wanda zai iya hana ruwa isa bisa fatarsa,amma bai sani ba  shin wannan abin kafin ya yi alwalla yake ko abayan ya yi alwalla ya same shi, anan alwallarsa ta inganta.Amma idan ya san cewa loakcin alwallar hankalinsa ba ya nan ta  yadda zai gane cewa shin akwai wannan abin ko babu,anan ya sake alwalla shi ya fi.

Mas’ala ta 303:Idan mutum bayan ya gama alwalla sai ya yi shakka a kan cewa shin a lokacin da yake alwalla wani abu mai hana ruwa isa zuwa fatarsa ya kasance ko bai kasance ba bisa gabban alwalla,Sannan yana  zaton cewa lokacin alwalla hankalinsa yana nan ta yadda sauran mutane zasu iya gasgata hakan, anan alwallarsa ta inaganta.

Baya kanu Gaba