Home Page
 Tarihin rayuwarsa
   Akidojin Shi'a
   Littafansa
   Fatawoyi
   Sakonni
   Darussa
   Littafan dansa
   Dakin karatu
   Hotuna


Affiliate Websites
Affiliate Websites

   E-Mail Listing:


 

Rabe-Raben Mata masu Haila:

Mas'ala ta 474:Mata masu haila sun kasu zuwa gida shida:

Ta daya:Wadda take da lokaci tsayayye da kuma kwanaki tsayayyu,wannan kuwa ana gane shi ne idan ta jera watanni biyu tana ganin jinni a lokaci guda kuma kwanaki tsayayyu.Kamar misali ya kasance tana farawa daya ga wata zuwa bakwai ga wata,idan ta maimaita wannan sau biyu ya zama al'adarta.

Ta biyu:Wadda take da tsayayyen lokaci kawai,amma kwanaki mabambanta,Ita wannan tana gane haka ne ta hanayr maimaita hakan sau biyu, misali kowane wata ta fara daya ga wata amma na farko ta yi kwana biyar na biyu kuwa ta yi kwana bakwai.

Ta uku:wadda take da kwanaki tsayayyu, shima wannan ana gane shii ta hanyar maimaita hakan sau biyu,wait ya zamana wata nafarko ta yi kwana shida na biyu ma ta yi hakan. Ammaa lokutta mabambanta, misalai wannan watan ta fara daya ga wata amma wata mai bi masa ta fara  biyar ga wata.

Ta hudu:wadda take ba ta da tsayayyen lokaci haka nan ba ta da tsayayyum kwanaki.wato tana iya faraway kowane llokaci sannan babu kwanaki tsayayyu da zata gama.

Ta biyar:Macen da ta fara ganin jinin haila a lokacin na farko.

Ta shida:macen da take manta al'adarta,wato takan manta kwana nawa take yi haka nan nawa ga wat take farawa,duktakan manta.Saboda wadan nan rabe-raben da muka ambata zamu fadi hukuncin kowane anan gaba kadan.

Mai tsayayyen lokaci da kwanaki:

Mas'ala ta 475:matan da suke haka sun kasu kashi uku:

Ta daya:Matar da ta ga jinin haila sau biyu cikin lokaci tsayayye a kwanuka tsayayyu.

Ta biyu:Matar da ta kasance jinin ba ya yankewa amma, amma jinin da yake da alamomin haila yakan tsaya bayankwanaki tsayayyu. Misali wata biyu a jere daga farkon wata zuwa bakwai jinin yana da almomin haila amma daga nana bin ya yi gaba,ya kan canza kala, amma baya yanke wa, kamar yadda muka fada a baya idan ya canza, daga nan zata dauka istihala ne.

Ta uku:Matar da taga  jinni a wata biyu a jere a lokaci guda,amma bayan kwana uku, sai jininta ya yanke, sannan sai ya sake dawowa, amma tsakanin na farko da na biyu bai wuce kwana biyu ba,Idan ya zamana ta maimaita wannan sau biyu,sannan ya zamana kwanakin da ta yi babu banbanci tsakanin na farko da na biyu.Amma anan  ba dole ba ne ya zamana kwanakin da ke tsakainin jini na farko da na biyu su zama sun yi dai-dai, muhimmi anan shi ne ya zamana kwanakin da ta kasance a cikin jinni yawansu ya kasance duk daya ne tsakanin wata na farko da na biyu.misali ya kasance bayan kwana uku sai jini ya yanke sai bayan kwana biyu sai ya sake dawowa,sannan ya dauki kwana uku sannan ya yanke baki daya, haka nan wata na biyu shi ma kamar haka, wato ya zamana baki dayan kwanakin kwana shida ne,duka wata  biyun.

Mas'ala ta 476:Matar da take da la'ada ta lokaci da kwanaki, idan tag a jinin a lokacin al'adarta ko kuma kwana biyu ko uku kafin lokacinta wato kafin lokacinta ya yi kenan ko kuma wasu kwanaki bayan lokacin da ta saba yi, anan koda jinin ba ya da alamomin jinin haila dole ne ta yi aiki da hukuncin mai haila,haka nan idan bayan wasu kwanaki sai ta fahimci cewa ba jinin haila ba ne, wato bai kai kwana uku ba sai ya katse,anan dole ne ta rama ibadar da ba ta yi ba  a cikin wadan nan kwanakin.

Mas'ala ta 477:Macen da take da al'ada ta lokaci da kwanaki,Idan tag a jini kafin lokacinta ya yi sannan kuma ya cigaba har zuwa lokacin da ta saba yi sannan ya wuce kwanakin da take yi, idan dai kwanakin duka bas u wuce kwana goma ba, zata dauke su duka a matsayin haila.Amma idan kwanakin suka wuce kwana goma,anan jinin da ta gani a kwanakinta na al'ada  su kadai ne  na haiala,saurankuwa istihala ne,sannan dole net a rama ibadar da ba ta yi ba a cikin kwanakin kafin hailer da bayan hailarta.

Mas'ala ta 478:Matar da take da al'ada lokaci da kwanaki, idan tag a jini a cikin kwanakin hailarta da wsu kwanki kafin hailarta, sannan duka bas u wuce kwana goma ba dukansu haila ce,amma idan sun wuce kwana goma,anan sai ta dauki kwanakinta da kwanakin da ta fara ganin jinin kafin lokacin al'adarta idan sun kai yawan kwanakin al'adarta sai ta dauke su matsayin al'adarta sauran kuma da suka karu a sama sai ta dauke su a matsayin istihala.Amma idan duka ba su wuce kwana goma ba sai ta dauke su duka a matsayin haila.

Mas'ala ta 479:matar da take da al'ada idan bayan kwana uku sai jinin hailarta ya yanke,sai kuma ya sake dawowa,sannan tsakanin na farko da na biyu ba su kai kwana goma ba,sannan duka kwankin da ta ga jini da wadan da jinin ya yanke ba  su fi kwana goma ba, anan yana da fuska guda hudu kamar haka:

1-Dukkan jinin da ta gani a lokaci na farko, ko kuma wani bangare daga ciki ya shiga cikin kwanakin al'adarta,sannan jinin da ta gain bayan jini na farko ya yanke bayankwankin al'adarta ya sake dawowa,anan sai ta dauki dukkan jini na farko a matsayin na al'adarta,wanda kuma ya zo na biyun sai ta dauke shi a matsayin istihala.

2-Jini na farko bai kasance a cikin kwanakin al'adarta ba,sannan dukan na biyu ko kuma wani bangare daga ciki ya kasance cikin kwanakin al'adarta,anan dole net a dauki dukkan jini na biyu a matsayin haila na farko kuwa a matsayin istihala.

3-Wani bangare daga  na farko da na biyu sun kasance cikin kwanakin al'ada, sannan a cikin kwanaki na farko bas u gaza kwana uku ba daga cikin kwanakin al'adarta, Sannan tsakanin yankewar jini na farko da na biyu bai kai kwana goma ba,anan duka kwanakin na haila ne.Amma kwanakin dab a su kasance ba cikin kwanakin al'ada a cikin kashui na farko, istihala ce,haka nan bangaren day a fita daga cikinkwnakin al'ada a cikin jini na biyu.misali idan mace ta kan ga jini daga uku ga wata,amma sai wani wata ta ga jini tun farkon wata zuwa shida ga wata ta ga jini,sannan sai jini ya yanke tsawon kwana biyu,sannan sai ta cigaba da ganin jini har zuwa sha biyar ga wata, anan daga uku ga wata zuwa goma ga wata jinin haila ne,sannan daga goma zuwa sha biyar na istihala ne.

4-Wani bangare daga cikin na farko da na biyu sun kasance a cikin kwanakin al'ada,amma kwanakin da suka kasance a cikin kwanakin al'ada daga cikin kashi na biyu ba su kai kwana uku ba,anan tsakanin jini na farko da na biyu dole ne ta bar duk abin da mai haila ba ta yi kamar yadda muka yi bayani a baya,Sannan ayyukan ibada da suke wajibi sai ta  yi aiki da hukuncin mai istihala kamar yadda muka fada a baya.

Mas'ala ta 480:Matar da take da al'adar lokaci da kwanaki,Idan ba ta ga jini ba a kwankin al'adarta,sai ta ga jini a wasu kwanki na daban, sannan dai-dai da yawan kwanakin da take yi,idan ya kasance bayan kwanakin hailarta ne,da ta ga jini kawai sai ta dauka hail ace, haka nan idan ta ga jinin kafin kwanakinta sannan yana da alamomin haial, sai ta dauke shi haila,amma idan ba shi da alamomin haila kuma bat a san cea ba shin zai kai kwana uku ko kuwa ba zai kai ba,anan har zuwa kwana uku zata guji ayyukan da suka haramata ga mai haila sannan dole ne ta aikata abubuwan suke wajibi, tare da yin amfani da hukuncin mai istihala.

Mas'ala ta 481:Matar da take da al'adar lokaci dakwanaki, idan ta ga jini a lokacin al'adarta, amma yawan kwanakin bas u kai yawan kwanakin al'adarta ba, ko kuma sun fi yawan kwanakin al'adar,sannan bayan wannan jinin ya yanke sai ta sake ganin wani jinin sannan yawansa ya yi dai-dai da yawan kwanakin al'adarta,anan ihtiyat wajib shi ne ta yi aiki da hukuncin mai haila sannan ta aikata abubuwan da suke wajibi a duka guda biyun.Sanan ta yi aiki da hukuncin mai istihala a wanann tsawon lokacin.

Mas'ala ta 482:Matar da take da al'ada ta lokaci da kwanaki, idan ta ga jini fiye da kwana goma,anan jinin da ta gani a cikin kwanakinal'adarta ko dab a shi da alamomin haiala shi zata dauka hailarta,amma jinin da zata gani bayan kwanakin al'adarta koda ya kasance yana da alamomin jinin haila jinin istihala ne.Misali matar da take ganin jini haila daya ga wata zuwa bakwai ga wata, sai ya kasnce tag a jinin fiye da kwana goma,anan daya zuwa bakwai kawai zata dauka matsayin haila, bakwai zuwa goma kuma istihala, koda kuwa wasu daga cikin daya zuwa na bakwai sun kasance ba su da alamomin haila,amma bayan bakwai ga wata  wasu daga ciki suna da alamomin haiala.Sai ta dauki wadan nan matsayin istihala.