Home Page
 Tarihin rayuwarsa
   Akidojin Shi'a
   Littafansa
   Fatawoyi
   Sakonni
   Darussa
   Littafan dansa
   Dakin karatu
   Hotuna


Affiliate Websites
Affiliate Websites

   E-Mail Listing:


 

Hukuncin likkafani

Mas'ala ta 564:Idan musulmi ya rasu wajibi ne a yi masa likkafani,wannan likkafani kuwa yana da bangarori guda uku,gyafto riga da mayafi.

Mas'alata 565:Gyafton kuwa dole ne ya kama daga cibiya zuwa kwauri,haka nan riga zata kama daga kafadu zuwa kwauri,amma mayafi kuwa zai kama tun daga saman kai har zuwa abin da ya rufe kafafu, sannan dole ne ya kasance mai fadi ta yadda za linka shi  a daure.

Mas'ala ta 566:Idan ya kasance magadan mamaci baligai ne kuma sun amince a yi masa likkafani fiye da wanda muka fada na wajibi, anan ba matsala ana iya amfani da dukiyarsa don yi masa likkafani na mustahabbi wato fiye da wanda muka fada a sama.Amma ihtiyat wajib shi ne kada a yi amfani da kason wanda ba baligi ba daga cikin magadan.

Mas'ala ta 567:Idan mamaci ya yi wasiyya ayi amfani da dukiyarsa don yi masa likafani fiye da na wajibi, sannan abin da ya yi wasiyyar ya kai daya bisa uku na dukiyar da ya bari, anan babu wani abu ana iya mafani da abin da ya yi wasiyyar da shi.

Mas'ala ta 568:likkafanin mata yana akan mijinta, hakan idan mutumn ya sakimatarsa sai ta mutu kafin ta cika idda, sannan kuma sakin wanda zai iya maido ta ne wato ba saki uku ba ne da makamantansa,anan likkafaninta yana a kansa.haka nan idan mijin ya kasance yaro ne wanda bai balaga ba, ko kuma ba shi da hankali, anan likkfanin ya hau kan wanda yake waliyyinsa.

Mas'ala ta 569:Yin likkafani bai zama wajibi ba ga dangin mamaci, koda kuwa sun kasance suke daukar nauyinsa kafin ya rasu.

Mas'ala ta 570:Ihtiyat wajib shi ne kada yadin da za a yi wa mutum likkafani ya zamana ba ya da kauri ta yadda za a iya ganin jikinsa.

Mas'ala ta 571:Dole ne likkafani ya kasance na halas,ko da dukiyar wanda ya amince a yi masa likkafanin.

Mas'ala ta 572:Bai halitta ba a yi wa mutum likkafani da abin da yake na haram.Don haka Idan a ka yi wa mutum likkafani da abin da ba na halas ba, dole ne a tono shi domin a canza masa wannan likkafanin.

Mas'ala ta 573:Bai halitta ba a yi wa mutum likkafani da fatar dabba mushe,amma idan ba a samu wani abin da za a yi masa likkafani ba ana iya yi masa da wannan din ba matsala.

Mas'ala ta 574:Bai halitta ba a yi wa mutum likkafani da abin da yake najasa,hakan nan bai halitta ba ayi wa mutum likkafani da abin da yadin da aka saka da alhariri ko aka hada  da zinari,amma idan ya zamana ba yadda za a yi babu matsala.

Mas'ala ta 575:Bai halitta ba a yi wa mutum likkafani da yadin da aka saka daga gashin dabbar da namanta haramun ne a ci sa, amma ida aka jeme fatar dabbar da ake ci ana iya yin likfani da ita babu matsala,haka nan idan aka saka yadi da gashin dabbar da ake ci ana iya yi wa mutum likkafani da ita babu matsala,duk da cewa ihtiyat mustahab shi ne a kaurace wa hakan.

Mas'ala ta 576:Idan likkafani ya samu najasa daga mamacin ko kuma daga waninsa,idan zai yiwu a wanke najasar to sai a wanke ta,amma idan ba zai yiwu a wanke ba sai a yanke wurin da yake da najasar,haka nan idan an riga an saka shi cikin kabari,ya zamana fito dashi daga kabari don a wanke najasar zai zama kamar rishin girmamawa a gareshi, to ihtiyat wajib shi ne a yanke wurin da yake da najasar.Amma idan zai yiwu a fito da shi kuma babu wata matsala don sake wani likkafanin to hakan ya fi.

Mas'ala ta 577:Idan mutum ya mutu yana cikin haramin hajji ko umara shima kamar sauran mutane za a yi masa likkafani babu matsala don an rufe fuskarsa da kansa.

Mas'ala ta 578:Mustahabbi ne mutum ya tanaji  kafur da magarya wadan da za sanya wajen yi masa wanka tun yana da lafiya.