Home Page
 Tarihin rayuwarsa
   Akidojin Shi'a
   Littafansa
   Fatawoyi
   Sakonni
   Darussa
   Littafan dansa
   Dakin karatu
   Hotuna


Affiliate Websites
Affiliate Websites

   E-Mail Listing:


 

Hukuncin Sallar gawa

Mas'ala ta 588:yiwa maaci musulmi salla wajibi koda kuwa yaro ne,amma doole ne iyayen yaro ko kakanninsa daya daga cikinsu sukan ce musulmi,sannan kuma yaron ya zama ya cika shekara shida. Wato kasa da haka ba wajibi ba ne a yi masa salla.

Mas'ala ta 589:Ana yin sallar gawa bayan an gama yiwa mamacin wanka  likkafani da shafa kafur,saboda haka idan aka yi sallar gawa kafin a gama wadan nan abubuwan sallar ba ta inganta ba.

Mas'ala ta 590: Ba dole ba ne mutum ya yi alwalla ko wanka  don yin sallar gawa,haka ba dole ba ne sai tufafinsa yana da tsarki, haka nan koda tufafin ba na halas ba ne babu matsala,duk da cewa dole ne a kiyaye sauran abubuwan da ya wajaba a kiyaye a cikin salla.

Mas'akla ta 591: Dole mutum ya kalli alkibla yayin sallar gawa,haka dole ya sanya mamacin a gabansa ta yadda kan mamaci zai kasance a damar mai sallar kafafuwansa kuwa su kasance a hagun mai salla.

Mas'ala ta 592: Kada ya zamana wurin da mai sallar yake yana sama da wurin da mamacin yake ko kuma ya kasance kasa da shi.Amma idan ya saknce bambancin ba mai yawa ba ne babu komai.

Mas'ala ta 593: Kada ya kasance mai salla yana nesa da yawa daga mamacin,amma idan ya kasance ana yin sallar cikin jam'I ne don mutum ya yi nisa da gawar idan dai yana hade da sahu babu matsala.

Mas'ala ta 594: Wajibi ne masu sallar gawa su kasane suna fuskantar gawar,amma idan ya kasance tsawon sahu ya zarce tsawon mamaci ta yadda wasu daga cikin masallatan ba su saitin mamacin,anan ba wani abu sallarsu ta inganta.

Mas'ala ta 595: Kada wani abu ya kasance tsakani mamaci da masu salla,wato kamar wani bango ko labule,amma don mamacin ya kasance cikin akwati babu matsala.

Mas'ala ta 596: Dole ne al'aurar mamaci ta zama a rufe yayin sallar gawa,saboda haka koda ba a yi masa likkafani ba sakamakon rashi, dole ne a rufe al'aurarsa da wani da ya sawwaka yayin yi masa salla.

Mas'ala ta 597: Sallar gawa dole ne ta kasance daga tsaye,sannan mutum ya yi niyyar kusanci ga ubanguji yayin wannan salla,sannan dole ne ya ayyana  mamacin,misali yayi niyya kan cewa zan yi wannan salla ne ga wannan mamaci don neman kuanci ga Allah.

Mas'ala ta 598: Idan ba a samu wanda zai yi sallar gawar ba daga tsaye,sannan kuma bai zai yiwu ba a jira don a samu wanda zai yi sallar daga tsaye, wato idan aka yanke kaunar samun wanda zai yi daga tsayen, ana iya yi sallar daga zaune,Amma idan kaka samu wanad zai yi sallar daga tsaye bayan angama sallar kafin a rufe shi, dole ne wannan ya yi masa sallar daga tsaye.

Mas'ala ta 599: Idan mamaci ya yi wasiyya cewa ga wanda zai yi masa salla ihtiyat wajib shi ne wannan mutum ya nemi izini daga waliyyin mamacin, sannan shi ma waliyyin ihtiyat wajib shi ne wajibi ne ya ba da iznin.

Mas'ala ta 600:Makaruhi ne a yi wa mamci salla sau da yawa,amma idan mamacin ya kasance mai ilimi ne da takawa babu laifi yin hakan.

Mas'ala ta 601:Idan ka rufe mamaci ba tare da an yi ma salla ba, sakamakon mantuwa ne ko kuwa da gangan,ko kuwa bayan an rufe shi sai aka fahimci cewa sallar da aka yi masa ba ta inganta ba,anan har idan dai jikinsa bai kai ga lalacewa ba, ya wajaba a yi masa sallar akan kabarinsa,tare da kiayaye sharudda da ka fada a baya.

Yadda ake sallar gawa:

Sallar gawa tana da kabbara guda biyar,saboda haka idan  mutum ya yi kabbara guda biyar kamar haka sallarsa ta inganta:

1-Bayan  kabbara ta daya sai ya ce:

اَشْهَدُ اَنْ لا اِلهَ اِلاّالله وَاَنَّ مُحَمَّداً رَسوُلُ اللهِ
2-Bayan kabbara ta biyu:

اللّهُمَّ صَلّ على مُحَمَّد وَآلِ مُحَمّد

3-Bayan kabbara ta uku; :

اللّهُمَّ اغْفِر لِلْمُؤمِنينَ وَالْمُؤمِناتِ.

إ4-Bayan kabbara ta hudu:
اللّهُمَّ اغْفِر لِلْمُؤمِنينَ وَالْمُؤمِناتِ.Idan mace ce kuwa:

اللّهُمَ اغْفِر لِهذِهِ الْميِّتِ

5-Bayan kabbara ta biyar shi ke nan ya gama.

Duk da yak eabin da ya fi shi ne bayan kabbara ta farko ya ce:

اَشْهَدُ اَنْ لا اِلهَ اِلاّ اللهُ وَحْدَهُ لا شَريكَ لَهُ اِلهاً واحِداً أَحَداً صَمَداً فَرْداً حيّاً قيّوماً دائِماً اَبَداً لَمْ يَتّخذْ صاحِبَةً وَلا وَلَداً، وَاَشْهَدُ اَنَّ مُحَمَّداً عَبْدُهُ وَرَسوُلُهُ اَرْسَلَهُ بِالْهُدى وَدينِ الْحَقِّ، لِيُظْهِرَهُ عَلَى الدّينِ كُلِّه، وَلَوْكَرِهَ الْمُشْرِكوُن. بَشيراً وَنَذِيراً بَيْنَ يَدَىِ السّاعَةِ.

Haka nan abin  da ya fi bayan kabbara ta biyu ya ce:

اللّهُمَّ صَلّ عَلى مُحَمَّد وَآلِ مُحَمّد وَبارِكْ عَلى مُحَمّد وَآلِ مُحَّمَداً و ارحم محمّداً وَآلَ مُحمّد كَاَفْضَلِ ما صَلَّيْتَ وَبارَكْتَ وَتَرَحَّمْتَ عَلى اِبْراهِيمَ

وَآلِ اِبْراهِيمَ اِنَّكَ حَمِيدٌ مَجيدٌ وَصَلِّ عَلى جَميعِ الاَْنْبياءِ وَالْمُرْسَلِينَ.

Bayan ta uku sai ya ce:

اللّهُمَّ اغْفِرْ لِلْمُؤمِنينَ وَالْمُؤمِناتِ وَالْمُسْلِميِنَ وَالْمُسْلِماتِ الاَْحْياء مِنْهُمْ وَالاَْمْواتِ تابِعْ بَيْنَنا وَبَيْنَهُمْ بِالْخَيراتِ اِنّكَ عَلى كُلِّ شَىء قَدِيرِ.

..............................................................Haka nan bayan ta hudu sai ya ce:…………………..:

 اللّهُمَ اِنَّ هذَا الْمُسَجَّى قُدّ امَنَا عَبْدُكَ وَابْنُ عَبْدِكَ وَابْنُ اَمَتِكَ نَزَلَ بِكَ وَاَنْتَ خَيْرُ مَنْزوُل بِهِ اَللّهُمَّ اِنَّكَ قَبَضْتَ روُحَهُ اِلَيْكَ وَقَدِ احْتاجَ اِلى رَحْمِتَكَ، وَأَنْتَ غَنىُّ عَنْ عَذابِهِ، اللّهُمَّ اِنّا لا نَعْلَمُ مِنْه اِلاّ خَيْراً وَاَنْتَ اَعْلَمُ بِهِ مِنّا اللّهُمَّ اِنْ كانَ مُحْسِناً فَزِدْ فى اِحْسانِهِ وَاِنْ كان مُسيئاً فَتَجاوَزْ عَنْهُ وَاغْفِرْلَنا وَلَهُ اللّهُمَّ اجْعَلْهُ عِنْدَكَ فِى اَعلى عِلّيّين وَاخْلُفْ عَلى اَهْلِهِ فِى الغابِرينَ وَارْحَمْهُ بِرَحْمِتَكَ يا اَرْحَمَ الرّااحِمينَ.

Bayan kabbara ta hudu idan mce ce sai ya ce:

اللّهُمَ اِنَّ هذِهِ الْمُسَجَّاةَ قُدّ امَنَا اَمَتُكَ وَابْنَةُ عَبْدِكَ وَابْنَةُ اَمَتِكَ نَزَلَتْ بِكَ وَاَنْتَ خَيْرُ مَنْزوُل بِهِ اَللّهُمَّ اِنّا لانَعْلَمُ مِنْها اِلاّ خَيْراً وَاَنْتَ اَعْلَمُ بِها مِنّا اللّهُمَّ اِنْ كانَتْ مُحْسِنةً فَزِدْ فى اِحْسانِها وَاِنْ كانَتْ مُسيئةً فَتَجاوَزْ عَنْها وَاغْفِرْلَها اللّهُمَّ اجْعَلْها عِنْدَكَ فِى اَعْلى عِلّيّين وَاخْلُفْ عَلَى اَهْلِها فِى الغابِرينَ وَارْحَمْها بِرَحْمِتَكَ يا اَرْحَمَ الرّااحِمينَ.

Sannan sai mutum ya yi kabbara ta biyar shi ke nan ya gama.

Mas'ala ta 603: Dole mutum ya yi kabbara da addu'I'n ba tare tsakani ba ta yadda kada ya fita daga siffar salla.

Mas'ala ta 604: Wanda yake sallar gawa a cikin jam;I shi ma dole ne ya yi kabbara da addu'o'in da ake yi.