Home Page
 Tarihin rayuwarsa
   Akidojin Shi'a
   Littafansa
   Fatawoyi
   Sakonni
   Darussa
   Littafan dansa
   Dakin karatu
   Hotuna


Affiliate Websites
Affiliate Websites

   E-Mail Listing:


 

Mustahabban Sallar gawa

Masala ta 605:Abubuwa goma ne suke mustahabbi wajen sallar gawa kamar haka:

NA daya:Mustahhabi ne wanda zai yi sallar gawa ya kasance yana da alwalla ko wankan wajibi ko taimama,ihtiyat shi ne zai yi taimama yayin da ba ya da ikon wanka, ko kuma yana jin tsoron idan ya tsaya yi wanka ko alwalla zai iya rasa sallar.

Na biyu:Mustahabbi ne idan mamaci namiji ne, liman ya tsaya dai-dai ttsakiyarsa  amma idan mace sai ya tsaya saitin kirjinta.

Na uku:Mustahabi ne mutum ya fitar da takalmansa yayin da yake yin sallar gawa.

Na hudu:Mustahabbi ne mutum ya daga hannunsa yayin kowa ne takbiri.

Na biyar:Mustahabbi ne mtutum ya tsaya kusa da gawar ta yadda da iska zai kada tufafinsa zai iya taba gawar.

Na shida:Mustahabbi ne mtum yayi sallar jana'iza a cikin jam'i.

Na bakwai:Mustahabbi ne liman ya daga muryarsa yayi da yake karanta addu'a,amma sauran mamu su yi a hankali.

Na takwas:Yayin sallar jana'iza a cikin jam'i koda mutum biyu ne dayan zai tsaya a bayan liman ne.

Mustahabbi ne mai sallar jana'iza ya yi wa mamacin addu'a da yawa da sauran muminai.

Na goma:mustahabbi ne kafin mutum ya fara sallar ya ce assala sau uku.

Na sha daya:mustahabbi ne ayi sallar gawar a wurin da mutane sukan cewa a can ne a yin sallar gawa.

NA sha biyu:Mustahabbi ne macemai haila idan zata yi sallar gawa, ta tsaya ita kadai a bayan sahu.

Mas'ala ta 606:Yin sallar gawa a cikinmasallaci makaruhi ne,amma  amma a cikim masallacin Ka'aba ba makaruhi ba ne.

Hukuncin rufe mamaci:

Mas'ala ta 607:Wajibi ne a rufe mutum ta yadda warinsa ba zai fito waje ba,Haka nan dole a rufe shi ta yada wasu dabbobi ba zasu iya tono shi ba,anan koda ba gudun cewa akwai muatane a kusa ta yadda idan da ba a rufe shi da kyau ba zai iya yiwuwa su cutu dag warinsa, ko kuma ba a tsammanin cewa za'a iya samun wata dabba wadda zata iya tono shi,anan ma ihtiyat shi ne a rufe shi da kyau kamar kwatankwacin yadda ana tsoron hakan.

Mas'ala ta 608:Idan da an rasa wurin da za'a gina a rufe mutum,anan ana iya rufe shi ta hanyar a kwaba kasa yabe shi,ko a sanya shi a cikin akwati a kwaba kasa a yabe.

Mas,ala ta 609:Za a rufe maamci ne ta hanyar a kwantar da shi bisa hannun dama sannan yakalli kibla.

Mas,ala ta 610:Idan mtumya mutu a ciki jirgin ruwa kuma ta yadda jikinsa ba zai lalace ba,sanan kuma zai iya yiwuwa a yi hakuri har fita daga ruwa,sannan a rufe shi a bisa kasa.Amma idan ya kaance  jikinsa zai iya lalacewa kafin a fita wajen ruwan,anan sai a yi masa dukkan abin dake yi wa mamaci,sannan sai daura dutsi  kafarsa sai saka shi jikin ruwan,sannan za a saka shi wajen da babu dabbobin da zasu ci namansa da sauri.

Mas'ala ta 611:Idan aka ji tsoron kada makiya su tono mamaci daga kabari su wulakanta gawarsa anan ana iya saka shi cikin kogi kamar yadda muka yi bayani a baya.

Mas'ala ta 612:Kudin da za a yi amfani da su wajen saka mamaci a cikin kogi ko gyara kabarinsa da makamantansa idan zai yiwu ana iya dauka a cikin dukiyar da ya  bari.

Mas'ala ta 613:Idan mace kafira ta mutu kuma ta mai ciki,sannan dan da yake ciki cikinta shima ba shi da rai,idan baban yaron ya kasance musulmi ne,anan dole ne kwantar da ita ta kalli bayan alkibla ta yadda fuskar yaron zata kalli alkibla.Koda kuwa ba a kai ga busa masa rai ba. ُُ

Mas'ala ta 614:Bai halitta ba a rufe musulmi a makabartar musulmi kamar yadda bai halitta a rufe kafiri a makabartar musulmi ba .

Mas'ala ta 615:Bai halitta ba a rufe musulmi a wurin da yake zai iya zma rishin girmamawa a gare shi kamar inda ake zubar da shara da makamantansu.

Mas'ala ta 616:Bai halatta ba a rufe mamaci a wurin da aka kwata,haka nan bai halitta ba a rufe mutum a wurin da aka ware don yin wani abu na musamman kamar masallaci ko wani wurin taro ko kuma wurin da aka ware don rufe wasu mutane na musaman wato ba na mutane gaba daya ba ne.

Mas'ala ta 617:Bai halitta ba a rufe mamaci a cikin kabarin wani ba,sai dai idan wanda aka riga a rufe a wurin ya riga ya zama kasa ta yadda hatta kasusuwansa  ba'a gani.saboda haka idan ana  tsammani cewa akwai yiwuwar cewa wanda aka rufe a wajen har yanzu bai zama kasa ba wato akwai yiwuwar akwai sauran kasusuwansa,anan bai halitta ba a tone kabarin don rufe wani a wajen.Kai bai ma halitta ba a tone kabari, sai dai idan kabarin ya tone da kansa a nan ana iya rufe wani a wajen wancan na farko idan  ya zama kasa babu sauran koda kasusuwansa.

Mas'ala ta 618:Abin ya cire daga jikin mamaci koda gashinsa ne ko farce ko  hakora, dole ne a hada da shi a rufe yayin bisne sa.Amma idan wadan nan abubuwan da muka ambata a sama sun rabu daga jikinsa ne lokacin da yake raye anan ba wajibi ba ne amma mustahabbi ne a rufe su tare da shi.

Mas'ala ta 619:Idan mutum ya mutu a cikin rijiya,sannan fito da shi ba zai yiwu ba,anan sai a rufe wannan rijiya ta zama kabarinsa.

Mas'ala ta 620:Idan jinjiri ya mutu a cikin cikin mahaifiyarsa,sannan kuma barinsa a cikin cikin mahaifiyar yana da hadari wato zai iya zama barazana ga rayuwarta,anan dole a bi hanya mafi sauki domin fito da shi daga ciki,koda ya zama dole a yi masa guntu-guntu babiu laifi akan hakan.Amma wanan aikin mijinta ne zai yi sa idan yana iya wa idan kuwa ba zai iya ba sai wata mata wadda ta san wannan aikin ta aiwatar da shi,Idan kuwa ba a samu wata mace ba wadda zata ita wannan aikin sai a samu wani namiji daga cikin maharramanta ya aiwatar da hakan,Idan kuwa ba a samu wanda zai iya ba daga cikin maharramanta, wanda ba maharraminta wanda ya san aikin yana iya  fito da dan,Idan kuwa ba a samu wanda ya san aikin ba anan koda wanda bai san aikin ba  yana iya fito da dan domin kasancewar barinsa a ciki yana da hadari ga ita uwar yaron.

Mas'ala ta 621:Duk loakcin da uwa ta mutu alhali akwai jinjiri mai rai a cikin cikinta,koda babu tabbas kan cigaba da rayuwar jinjirin anan sai a fasa cikin ta bangaren hagu a fito da jinjirin sannan a maida a dinke cikin.