Home Page
 Tarihin rayuwarsa
   Akidojin Shi'a
   Littafansa
   Fatawoyi
   Sakonni
   Darussa
   Littafan dansa
   Dakin karatu
   Hotuna


Affiliate Websites
Affiliate Websites

   E-Mail Listing:


 

Mustahabban rufe mamaci

Mas'ala ta 622:Mustahabbi ne a yi kabari dai-dai tsawo da fadin mutum matsakaici,sannan mustahabbi ne a rufe mutu a makabarta mafi kusa, sai idan idan makabartar da take nesa a akwai wani dalili wanda ya sa za a iya kai mutum a can,kamar idan ya zamana a makabartar mutane sun fi zuwa ziyara don yi wa mamata addu'a, ko kuma saboda ana rufe manyan bayin Allah a wurin. Mustahabbi ne bayan an saka mutum a cikin kabari a kwance dauri da aka yi wa likkafanin,sannan a dangana fuskarsa ga bangon kabari a sanya wani abu a bayansa ta yadda kada ya dawo baya.Sannan kafin a rufe mamaci sai a kama kafadarsa ta dama da hannun dama sannan kafadar hagu da hannun hagu sannan a girgiza shi sannan a ce ya kai wane dan wane,Sannan sai a karanta wannan addu'ar…….

Mas'ala ta 623: Mustahabbi ne wanda zai saka mamaci a cikin kabari ya kasance ya tube takalmansa sannan ya zama kansa a bude,sannan ya kasance yana da alwalla.haka nan idan zai fito daga kabari sai ya fito ta bangaren kafafun mamacin,Sanana idan akwai wasu daga cikin wadan da suka halarci jana'izar wadan da ba su daga cikin dangin mamacin idan zasu iya, sai su tura kasa da bayan hannunsu su rufe mamacin suna masu cewa…… Idan mamacin ya kasance mace ce,wanda zai shiga cikin kabari ya zamana daya daga cikin maharramanta wato wadan da suke danginta na kusa wadan da ba zasu iya aurenta ba.Idan kuwa ba a samu daya daga cikin wadan nan ba sai wani daga cikin dangi ya saka ta cikin kabarin.

Mas'ala ta 624:Mustahabbi ne a gina kabari ta yadda tsawonsa  ya fi fadinsa (Triangle), sannan ya tasa sama kamar tsawon yatsa hudu daga kasa,sannan a sanya alama a bisa kabarinsa ta yadda kada ya bata,sannan bayan an gama rufe mamacin sai a fesa ruwa a sama sannan mutane daga suka halarci rufe mamacin su dora yatsunsu bisa kabarin su karanta masa Inna anzalnahu kafa bakwai sannan su nemar wa mamacin gafarar Allah madaukaki, sai su karanta wannan addu'ar:…

Mas'ala 625:Bayan wadan da suka halarci jana'izar sun tafi mustahabbi ne waliyyin mamaci ko wanda yake da izini daga waliyyinsa ya tsaya ya karanta masa addu'o'in da ake wa mamaci.

Mas'ala ta 626:Mustahabbi ne a yi wa wadan da aka yi wa mutuwa gaisuwa amma idan lokacin ya wuce don kada a tado masu abin, bai kamata ba a yi masu gaisuwar.Sannan mustahabbi ne a aika abinci zuwa gidan mutuwa har tsawon kwana uku,sannan makaruhi ne a ci abinci a gidan mutuwa har tsawon kwana uku,(wato ga wadan da  ba 'yangidan ba)

MAs'ala ta 627:Mustahabbi ne mutum ya yi hakuri yayin da wani daga cikin danginsa ya mutu musamman idan dansa ya mutu sannan idan ya tuna wanda ya mutu sai ya ce Inna lillahi wa'inna ilahi raji'un, sannan mustahabbi ne a karanta wa mamaci kur'ani sannan mutum yana iya neman biyan bukatunsa daga Allah madaukaki a kan kabarin Iyayensa,sannan mustahabbi ne a gyara kabari da kyau ta yadda ba zai yi saurin lalacewa ba.

Mas'ala ta 628:Bai halitta ba sakamakon rasuwar wani daga cikin dangi, mutum ya yage jikinsa saboda bakin ciki.

Mas'ala ta 629:Haka nan bai halitta ba mutum ya yaga kayansa sakamakon mutuwar wani idan ba babansa ba.

Mas'ala ta 230:Idan mutum sakamakon mutuwar dansa ko matarsa ya yaga kayansa,ko kuma sakamakon mutuwar wani, mace ta ji wa kanta ciwo,ta yadda jini ya fita, ko kuwa ta tsige gashinta,anan dole ne  mutum ya yantar da bawa,ko kuma ya ciyar da mabukata goma,ko kuma ya yi masu tufafi,Idan kuwa ba zai iya aiwatar da wannan ba sai ya yi azumi guda uku.Ihtiyat koda jini bai fito ba sai mutum ya bayar da abin da aka fada a sama.

Mas'ala ta 631:Ihtiyat wajib kada mutum ya daga murya sama da karfi yayin kukan mutuwa.

Sallar wahasha

Mas'ala ta 632:Mustahabbi ne daren da aka rufe mamaci a yi masa sallar wahasha,wannan salla kuwa raka'a biyu ce,a raka'a ta farko ana karanta Ayatul kursiyyi bayan Fatiha,a raka'a ta biyu kuwa ana karanta Inna anzalnahu,sannan bayan an yi sallama sai a karanta  wannan addu'ar…….

Mas'ala ta 633:Ana iya yi sallar wahasha a kowane lokaci bayan rufe mamacin da daddaren ranar,amma abin da ya fi shi ne a yi sallar a wannan daren da aka rufe shi.

Mas'ala ta 634:Idan ana so a kai mamaci wani gari don a rufe shi  a can  ko kuwa saboda wani dalili ana so a jinkirta rufe shi,anan sai a jinkirta yi masa wannan sallar har zuwa daren da aka rufe shi.

Tone kabari

Mas'ala ta 635:Haramun ne a tone kabarin musulmi koda kuwa karamin yaro ne ko mahaukaci,amma idan jikin mamacin ya zama kasa babu laifi don an tone shi.

Mas'ala ta 636:Haramun ne  a tone kabarin Manyan bayin Allah koda kuwa ya dauki tsawon shekaru kamar yadda muka fada a sama.

Mas'ala ta 637:Halas ne a tone kabari a wadan su lokutta kamar haka:

Na daya:Idan aka rufe mamaci a wani wuri  sai mai wajen bai amince ba.

Na biyu:Idan ya zamana likafanin da ka rufe mamaci da shi ba na halas ba ne,sannan kuma mai shi bai aminta ba,ko kuwa idan aka rufe mutum da dukiyar da ya kamata ya bar wa masu gadonsa,sannan kuma  masu gadon ba su aminta da  a bar dukiyar ba,amma idan mutum ya yi wasiyya akan a rufe shi  da wani kur'ani ko zobe,sannan abin bai kai yawan daya bisa uku na dukiyarsa ba anan ba sai an tono shi ba.

Na uku:Idan aka rufe mamaci ba tare da an sanya masa likkafani ko an yi masa wanka ba ko kuma aka fahimci cewa wankasa bai inganta ba, ko kuwa an sanya masa likkafani ba kamar yadda shari'a ta bayyana ba,ko kuwa ba a sanya shi cikin kabari ba kamar yadda ya kamata a sanya shi, kamar a sanya shi bai  kalli kibla ba,amma anan  ma sai idan tone kabari ba zai zama keta alfarmar mamacin ba,amma idan zai zama keta alfarmarsa kamar a samu jikinsa ya riga ya lalace ko wani abu makamancin hakan,anan bai halitta ba a toneshi.Amma idan aka rufe mutum ba a yi masa salla ba,anan bai halitta ba a tone kabarinsa don a yi masa salla,anan ana  iya yi masa salla akan kabarinsa.

Na hudu:Idan za a tone mamaci ne domin a tabbatar da wani abu kamar binciken likita idan ana so a tabbatar da wani  abu a kansa.

Na biyar:Idan ka rufe musulmi a wani wuri inda yake kamar rishin girmama wa ne garesa kamar idan an rufe sa a makabartar kafirai ko wurin da ake zubar da kazanta, anan ana iya tono shi domin a maida shi makabartar musulmi.

Na shida:Idan za'a aiwatar da wani abu wanda yake muhimmi kamar a na so a ceto jinjirin  da yake cikin cikin macen da ta mutu,kuma dan yana da rai.

Na bakwai:Idan aka samu wani bangaren jikin mamaci bayan an riga na rife shi kamar sakamakon hadari sai wani bangare jikinsa ya bata sai aka gane shi daga baya,anan ana iya tone kabarinsa don a hada a rufe.

Na takwas:Idanb ana jin tsoron kada wasu dabbobi su tone gawarsa su cinye.

Na tara:Idan mutu ya yi wasiyya akan cewa akai shi wuri mai tsarki a rufe,sai aka manta ko kuma da gangan a ka rufe shi a wani wuri daban,anan  anan iya tone shi don a kai shi inda ya yi wasiyya  a rufe shi a can.Amma idan tone shi zai zama kamar keta alfarmarsa wato jikinsa ya riga ya fara lalacewa anan bai halitta ba a tone shi.