Home Page
 Tarihin rayuwarsa
   Akidojin Shi'a
   Littafansa
   Fatawoyi
   Sakonni
   Darussa
   Littafan dansa
   Dakin karatu
   Hotuna


Affiliate Websites
Affiliate Websites

   E-Mail Listing:


 

Taimama

Taimama tana wajaba a wurare guda bakwai wato maimakon alwalla ko wanka dole ne a yi taimama.

Wuraren da ake yin taimama:

NA DAYA:Lokacin da mutu ba zai iya samun rowan dazai yi alwalla ko wanka ba.

Masßla ta 642:Idan mutum yana wurin da za a iya samun ruwa,anan dole ne mutum ya yi iya kokaronsa wajen neman ruwan da zai alwalla ko wanka sai idan ya yanke kauna akan cewa lallai ba zai samu ba.Idan mutum ya kasance a cikin daji inda yanayin wurin yana tudu da kwari ta yadda ba zai yiwu ba mutumya yi tafiya cikin jin dadi,anan sai mutum ya yi tafiya kowane bangare tsawon nisan idan da za a harba kibiya zata iya zuwa wurin.Wato ya yi tafiya gabas da yamma kudu da arewa,idan bai samu ruwa ba sannan ya yi taimama.

Masßla ta 643:Idan ya zamana wurin da mutum ya samu kansa yana da tudu da gangara, ko kuma tafiya don neman ruwa yana da wuya a garesa,anan sai ya ya yi tafiya kamar nisan harbin kibiya a wurin da yake ba ya da hawa da gangara,sannan ya yi kimanin hakan a wurin da yake da hawa da gangara.

Mas'ala  ta :644:Duk wurn da mutum yake da tabba s ba za a samuruwa ba,anan ba dole ba ne ya yi tafiya kamar kimanin da muka fada a sama.Anan kawai yana iya yin taimamarsa.

Mas'ala ta 645:Idan lokacin salla bai kure ba kuma mutum yana da yakini akan cewa zai samu ruwa kafi lokacin salla ya kure,anan dole ne ya yi kokari ya binciki ruwan idan har babu wani abu da zai hana yin hakan kuma ba zai zama wahalarwa ba,amma idan mtum Kawai yana tsammani ne kan samun ruwan,anan ba dole ba ne ya tafi neman ruwan koa kuwa lokaci bai kure ba.Amma idan mutu ya natsu akan cewa zai samu ruwa a wani wuri anan ihtiyat wajib shi ne ya ta fi wajen don ya samo ruwan da zai yi alwalla.

Mas;ala ta 646:Ba dole ba ne mutum ya tafi da kansa don ya nemo ruwan da zai yi alwalla,idan ya tura wani ma don ya samo masa ya wadatar.Saboda haka idan mutum daya ya tafi don  ya samo wa mutane da yawa ruwan da zsu yi alwalla hakan ya inganta.

Mas'ala ta 647:Idan mtutm ya yi tsammanin cewa a cikin kayansa da yake tare da su yayin tafiya akwai ruwa ko kuma a cikin gidansa,anan dole ne ya yi bincike ta yadda zai tabbatar da akwai ko babu,ko kuma ya yanke kauna daga samun ruwan.

Mas'ala ta 648:Idan mutum tun kafin lokacin salla ya isa ya nemi ruwa kuma bai samu ba,sanna kuma bai bar wurin da yake ba har lokacin salla ya isa,anan ba dole ba ne ya sake binciken ruwan don ya yi alwalla.

Mas'ala ta 649:Idan mutum ya nemi ruwa don yin alwalla lokacin da salla ya isa,kuma sai bai samu ruwan ba,anan idan bai bar wannan wurin ba har wani lokacin sallar ya sake yi, anan ba sai ya sake neman ruwan ba.Amma idan yana tsammanin cewa za iya samun ruwan anan ihtiyat wajib shi ne ya sake bincikawa.

Mas;ala ta 650:Idan mutum ya ji tsoron wata dabba mai cutarwa ko barawo ko kuma akwai wahala mai tsanani akan neman ruwan anan ba dole ba ne ya nemi ruwa don ya yi alwalla.

Mas'ala ta 651:Idan mutum bai tafi neman ruwan da zai yi alwalla ba har sai da lokacin salla ya kure anan yana iya yin salla da taimama kuma sallarsa ta yi amma kuma ya yi zunibi akan rishin neman ruwan da ya yi.

Mas'ala ta 652:Wanda ya samu tabbas akan cewa ba zai samu ruwa ba,sai ya yi salla da taimama ba tare da ya nemi ruwan ba,amma bayan ya yi sallar sai ya fahimci cewa idan da ya binciki ruwan da ya samu,anan sallarsa ta ba ci.

Mas'ala ta 653:Idan mutum  ya yi salla bayan ya binciki ruwa bai samu ba,bayan ya gama salla sai ya fahimci cewa a wurin da ya binciki ruwan bai samu ba akwai ruwa a wajen,anan sallarsa ta inganta.

Mas'ala ta 654:Idan mutum ya kasance yana da alwalla bayan lokacin salla ya shiga,sannan ya san cewa idan ya bata alwallarsa ba zai samu ruwan da zai sake alwalla ba,anan idan har zai ya rike alwallar dile ne ya rike ta har ya yi sallar.

Mas'ala ta 655:Idan mutu ya kasance yana da alwalla kafin lokacin salla ya isa,sanna ya san cewa idan ya bata alwallarsa ba zai samu wani ruwan da zai yi alwalla ba,anan idan zai iya rike alwallar ihtiyat wajib shi ne ya rike alwallar har lokacin salla ya isa don ya yi sallarsa da alwalla.

Mas'ala ta 656:Idan yana da ruwan da zai yi alwalla ko wanka kuma ya san idan ya zubar da wannan ruwan ba zai samu wani ba wanda zai yi alwalla ko wanka,anan idan lokaci salla ya isa ne haramun ya zubar da wannan ruwan da yake da shi,haka nan idan lokacin sallar bai isa ba,ihtiyat wajib shi ne kada ya zubar da wannan ruwan.

Mas'ala 657:Wanda ya ke da tabbas akan cewa ba zai samu ruwa ba,Bayan lokaxcin salla ya isa sai ya bata alwallarsa ko ya zubar da ruwaan da yake da shi, anan ya yi sabo,amma sallarsa da ya yi da taimama ta inganta,duk da cewa ihtiyat mustahab shi ne ya rama wannan sallar.