Home Page
 Tarihin rayuwarsa
   Akidojin Shi'a
   Littafansa
   Fatawoyi
   Sakonni
   Darussa
   Littafan dansa
   Dakin karatu
   Hotuna


Affiliate Websites
Affiliate Websites

   E-Mail Listing:


 

Wuraren da suke ba wajibi ba ne tufafin dq jikin mai salla ya zama mai tsarki:

Mas'ala ta 860: Wurare guda uku ne kamar yadda zasu zo idan mutum ya yi salla tare da jiki ko tufafin mai najasa bamatsala ku,kuma sallarsa ta inganta:

Na daya: idan ya zamana sakamakon ciwo ko kurji a jikin mutum sai jikinsa ko tufafinsa suka samu najasa da jini.

Na biyu:Idan bisa jikin mutum ko tufafinsa akwai akwai jini wanda girmansa bai wuce kan dan tyatsa ba,sai dai idan  ya kasance daya ne daga jininanen da zamu fada a ciin mas'ala ta 861.

Na uku:A inda ya zama dole mutum ya yi salla da tufafi mai najasa.

A wurare biyu kawai idan mutum ya yi salla da tufafi mai najasa sallarsa ta inganta.:

NA daya Idan ya zamana abin da yake da najasar karami ne safa ko safar hannu.

Na biyu:Idan ya zamana tufafin mai najsa na mace mai goyo ne,kamar yadda zamu fadi hukuncinsa a nan gaba ta fuskoki guda biyar.

Mas'ala ta 861: Idan ya zamana tufafin mai salla ko jikinsa ya samu jini ta hanyar ciwon da yake da shi,ta yadda wanke jinin ko canza wasu kaya zai zama wahala ga mutumin,Har ya zuwa lokacin da raunin zai warke mutum yana da uziri ya yi salla da wannan jinin da ya bata masa jiki ko tufafi.Haka nan idan jinin ya bata abin da aka daure ciwon da shi ko kuma maganin da yake a kan ciwon sai ya taba jikin mutum ko tufafinsa.

Mas'ala ta 862: Idan jinin ciwo karami wanda bai shiga cikin jiki ba sosai ya bata jikin mutum ko tufafinsa kuma yawansa ya kai ko ya dara kan dan yatsa, ta yadda wanke sa ba zai zama da wahala ba,idan mutum ya yi salla da shi sallarsa ta baci.

Mas'ala ta 863: Idan ya zamana wirin da yake da nisa tsakaninsa da inda yake da ciwo sai ya samu najar wannan ciwon,a nan bai halitta ba mutum ya yi salla da wannan najasar,amma idan ya zamana kusa da ciwon ne ta yadda ya kan taba lemar ciwon ko kuma idan tufafi ne ya kan taba ciwon, anan salla da shi babu matsala.

Mas'ala ta 864: Jinin da yake fitowa da dadashin mutum ko hancinsa ba su da hukuncin jinin ciwo,don haka idan daya daga cikin ya taba jiki ko tufafin mutum bai halitta ba ya yi salla da shi,sai dai idan yawansa bai kai girman dan yatsa ba.Amma jinin basir da yake fitowa ta duburar mutum yana da hukuncin jinin ciwo don salla da shi babu matsala.

Mas'ala ta 865: Mutum da yake da ciwo a jikinsa idan ya ga jinin a jikinsa ko tufafinsa,sannan ya kasa gane cewa shin wannan jinin daga ciwon ne ko kuwa wani jini ne daban,babu laifi yana iya yin  salla da shi babu matsala.

Mas'ala ta 866: Idan mutum yana ciwuka a jiki da yawa sannan kuma suna kusa da kusa,ta yadda za a iya cewa ciwo daya ne,har ya zuwa lokacin da zasu warke salla da jininsu babu matsala.Amma idan suna da nisa da juna ta yadda za a iya cewa ko wane daya daga cikin ciwo ne mai zaman kansa,don haka lokacin da daya daga cikinsu ya warke dole ne mutum ya wanke jinin wannan wanda ya warke din daga jikinsa ko tufafinsa kafin ya yi salla.

Mas'ala ta867:Idan jinin haila dai-dai da kan allura ya kasance a kan tufafin mai salla,idan ya yi salla da shi sallarsa ta baci.Sannan ihtiyat wajib bai kamata ba jinin biki ko na istihala su kasance bisa tufafin mai salla,sannan ya kamat a kaurace  wa jinin dabbar daq ba a ci,amma jinin dabbada a ke ci ko na mutum koda ya kasance a wurare da yawa ta yada idan da za a tattara shi wuri guda ba zai kai fadin kan dan yatsa ba,idan mutum ya yi sala shi babu matsala sallarsa ta inganta.

Mas'ala ta868:Jinin da ua zubabisa tufafin da ba ya da shafi sannan jinin ya isa zuwa bayan tufafin,za a lissafa wannan jinin na gaba da na baya matsayin jinin guda,amma idan ya kasance tufafi yana da shafi ta yadda bayan tufafin ya bambanta da gabansa, anan dole ne a lissafa kowa ne jinin daban.Saboda haka idan jinin da yake gaba da baya baki daya bai kai girmana kan danyatsa ba salla da shi babu matsala,amma idan an hada su duka gida biyu sun kai yawan kan dan yatsa a nan salla da shi ba ya inganta.

Mas'ala ta869:Idan jini ya zuba bisa tufafin da yake da shafi sannan jinin ya isa zuwa ga shafin,ko kuma jinin zuwa ne bisa shafin sannan ya isa har zuwa ga wajen tufafin,a nan idan duka jinin da yake bisa tufafin da wanda ya isa zuwa shafin tufafin ko kuma wanda yake bisa shafin da wanda yake bisa tufafin ba su kai girman kan dan yatsa ba babu matsala yin salla da shi kuma sallar ta inganta,ammam idan ya wuce haka salla da shi ba ya inganta.

Mas'ala ta870:Idan jinin da ya ke bisa tufafin ko jikin mai salla ya gaza wa girman kan dan yatsa,idan lema ta isa zuwa ga wannan jinin sannan jinin da lemar da ta taba shi sun kai girman kan yatsa,sannan wannan lemar ta bata gefen wurin,bai halitta ba mutum ya yi salla a haka idan mutum ya yi salla haka sallarsa ta baci.Kai kodama lemar da jinin ba su girmana kan dan yatsa ba kuma ba su bata gefen wurin da suke ba,salla da shi haka yana da matsala,amma idan lemar ta hadu da jinin ta yadda yanzu ba a ganin jinin idan mutum ya yi salla da shi babu matsala kuma sallarsa ta inganta.

Mas'ala ta871:Idan jilin mutum ko tufafinsa ba su baci da jini ba amma ta hanyar taba jini sai suka kasance masu najasa,a nan koda wurin da ya zama mai najasa bai kai girmana yatsa ba bai halitta ba a yi salla da shi ba.

Mas'ala ta872:Idan jinin da ya kasance a bisa tufafi ko jiki bai kayi girmana yatsa ba amma sai wata najasa ta taba wajen misali kamar fitari ya taba wajen.a nan bai halitta ba mutum y a yi salla da wannan tufafi ko jikin da ya samu wanna najsar.

Mas'ala ta873:Idan najasa ta taba daya daga cikin kanan tufafin mai salla kamar diko ko safa da makamantansu wato abubuwanda bai yiwuwa a rufe al'aura da su, sannan kuma ba an yi su ba ne daga fatar dabbar da take haram,a nan ya halitta mutum ya yi salla da su kuma sallarsa ta inganta.Haka nana idan mutum ya yik salla da gilashi ko zobe mai najasa sallarsa ta inganata.

Mas'ala ta874:Ihtiyat  wajib shi ne  kada mutum ya yi salla da abu mai najasa kuma wanda zai yiwu a rufe al'aura da shi,amma babu laifi don mutum ya yi salla da abu mai naja sa amma wanda ba zai yiwu ba mutum ya rufe al'aurarsa da shi ba, kamar hankici ko mabudi ko wuka masu najasa, haka babu laifi don mutum ya yi salla da kudi masu najsa.

Mas'ala ta875:Matar da take rainon yaro,ihtiyat wajib idan yaron ya kasance namiji kuma ba ta da tufafi fiye da guda daya idan ba zata iya sayen wani tufafin ba ko kuma ba zata iya aron wani ko ta amso haya ba,Idan ta wanke tufafin sau daya cikin tawon kwana daya koda kuwa yaron ya yi mata fitsari ne a rana ta biyu tana iya yin salla da wannan tufafin babu matsala.Amma ihtiyat wajib shi ne matar ta wanke tufafi sau daya a cikin kwana da yini,sannan ya kasance ta wanke tufafin ne a farkon sallar da zata yi bayan tufafin ya samu najasa.Haka idan ta kasance tana da fiye da tufafi guda amma dole ne ta yi amfani da su baki daya a lokacin sallar,saboda haka idan a tsawon kwana da yini ta wanke tufafin kamar yadda muka fada a sama ya wadatar.Amma idan tana iya sayen wani tufafin ko kuma ta amso haya,ihtiyat wajib shi ne ta yi salla a cikin tufafi masu tsarki.

Abubuwan da suke mustahabbi ne dangane da tufafi ga mai salla:

Mas'ala ta876:Musatahabbi ne sanya rawani tare da sako wutsiyarsa a gaba,haka nan an so mutum ya sanya abaya musamman limami,sannan musatahabbi ne mutum ya sanya fararen kaya yayin salla kuma suka kasance a cikin tsabta,Sannan mustahabbi ne mutum ya sanya turare kuma sanya zoben akik a dan  yatsansa yayin da yake salla.

Abubuwanda suke makaruhi dangane da tufafin mai salla:

Mas'ala ta877:Makaruhi ne mutum ya yi salla da bakaken kaya,haka nan makaruhi ne mutum ya yi salla da kaya wadan da suke sun matsa jinkin mutum,kuma makaruhi ne mutum ya yi salla da tufafin mai shan giya,Sannan makaruhi ne mutum ya sanya tufafin mutumuimin da bai kula ba da kiyaye najasa,haka nana makaruhi ne mutum ya sanya tufafi masu zanen hotuna, kuma makarihi ne mutum ya bude maballensa yayin salla,haka nan makaruhi ne mutum ya sanya zoben da yake da zanen hoto a hannunsa ya yin salla.